logo

HAUSA

Kasar Sin za ta goyi bayan Eritrea wajen kiyaye cikakaken ’yanci da martabarta

2022-01-06 09:55:55 CRI

Kasar Sin za ta goyi bayan Eritrea wajen kiyaye cikakaken ’yanci da martabarta_fororder_0106-WangYi-Faeza

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma minsitan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce kasarsa za ta taimakawa kokarin Eritrea na kare cikakken ’yanci da yankuna da kuma martabarta, tare da adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar da kakkaba mata takunkumi.

Wang Yi ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi da shugaban Eritrea, Isaias Afwerki. Eritrea ce wuri na farko da Wang yi ya yada zango a rangadinsa na kasashen Afrika 3. Zai kuma je kasashen Kenya da Comoros.

A nasa bangaren, shugaba Isaias ya yabawa dinbin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da kudurinta na adawa da danniya da gina tsarin adalci da daidaito a duniya. Ya ce nasarar kasar Sin ta kawo wa bil adama kyawawan fata da kwarin gwiwa ga kasashe masu tasowa. Yana mai cewa, yana sa ran kasar Sin za ta kara taka rawa wajen taimakawa ci gaban nahiyar Afrika.

Ya kara da cewa, Eritrea ta kasance mai goyon bayan kokarin kasar Sin wajen kare cikakken ’yanci da yankunanta da kuma halaltacciyar matsayarta. Kuma kasarsa ta shirya wani tsari na inganta hadin gwiwarta da Sin, kana tana sa ran zurfafa hulda a tsakaninsu a fannonin da suka shafi ababen more rayuwa da ma’adinai da aikin gona da horar da ma’aikata. (Fa’iza Mustapha)