logo

HAUSA

IOC ya bukaci dukkan mahalarta gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da su bi ka'idojin yaki da COVID-19 da aka tsara

2022-01-06 10:51:28 CRI

IOC ya bukaci dukkan mahalarta gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da su bi ka'idojin yaki da COVID-19 da aka tsara_fororder_0106-Olympics-Ibrahim

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa IOC, jiya Laraba ya gudanar da jerin taruka da wakilan 'yan wasa daga dukkan sassa na duniya, da kwamitocin wasannin Olympic na kasa da na shiyya, da kuma hukumar kula da wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta kasa da kasa, don gabatar musu ci gaban da aka samu a game da shirye-shiryen wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing.

Babban darektan sashen kula da wasannin Olympics na kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Christopher Dolby, ya bayyana cewa, tsarin kula da wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, ya fara aiki yadda ya kamata, kuma tsarin isa wurin shi ma yana tafiya ba tare da wata matsala ba. Ya kuma jaddada cewa, yanzu lokaci ne mai matukar muhimmanci, don haka, dole ne dukkan mahalarta gasar Olympics da za su je birnin Beijing, su yi taka tsantsan. Yana mai cewa, kafin su tashi zuwa birnin Beijing, ya kamata su bi matakan da aka zayyana a cikin littafin "rigakafin kamuwa da COVID-19 ta gasar Olympics da ajin nakasassu ta Beijing ta shekarar 2022". (Ibrahim Yaya)