Sin ba za ta kaucewa alkawuran ta na goyon bayan nahiyar Afirka ba
2022-01-06 15:43:29 CRI
Ga duk mai bibiyar al’amura da suka jibanci ci gaban da ake samu, don gane da dangantakar kasar Sin da sassan nahiyar Afirka, zai lura cewa, sassan biyu na da wata dadaddiyar alaka ta gargajiya, wadda a karkashin ta, sassan ke taimakawa juna, da goyon bayan juna, tare da kare muradun juna a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A matsayin Sin da kasashen Afirka na aminai, kuma kasashe masu tasowa, sassan biyu sun kafa wani tarihi na fahimtar juna, wanda ke ba su damar cin gajiya daga hadin gwiwar su yadda ya kamata.
Ana iya ganin karfin tasirin wannan dangantaka ta Sin da kasashen Afirka, ta hanyar duba ga nasarorin da suka cimma, karkashin dandalin nan na hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, da ma shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, wadanda dukkaninsu ke taka rawar gani, wajen bunkasa cudanyar sassan yadda ya kamata.
A bangaren kasar Sin, kasancewar ta babbar kasa mai karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, ta yi namijin kokari wajen tallafawa kasashen Afirka, da hanyoyin samar da manyan ababen more rayuwa, kuma a shekarun baya bayan nan, ta yi rawar gani wajen tallafawa kasashen nahiyar da alluran rigakafin cutar COVID-19, da kasashen Afirkan ke matukar bukata don yaki da wannan annoba.
Bugu da kari, ziyarar da kowane ministan harkokin wajen kasar Sin ke kaiwa sassan nahiyar Afirka, a farkon duk shekara cikin shekaru 32 kawo yanzu, ta daga nuna irin muhimmanci da Sin ke dorawa, ga sha’anin raya dangantakar sassan biyu.
A wannan karo ma, minsitan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya fara ziyara a Eritrea, kafin isarsa kasashen Kenya da Comoros. A Eritrea, Wang Yi ya jaddada manufar kasar Sin ta goyon bayan kasar a fannin kare cikakken ’yanci, da yankuna da kuma martaba kimarta, tare da adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, ko sanyawa kasar takunkumi.
Ko shakka babu, wadannan kalamai na Mr. Wang, sun kara yin nuni ga jajircewar kasar Sin, wajen tabbatar da goyon bayanta ga kawayenta na Afirka a dukkanin fannonin ci gaban su.
Wadannan dalilai ne kuma, suka sanya dukkanin masu kishin ci gaban Afirka, ke ganin a yanzu da ma nan gaba, kasashen nahiyar na da tarin alfanu da za su ci gaba da samu, karkashin wannan dangantaka mai dogon tarihi. (Saminu Hassan)