Ana daf da kammala dukkanin shirye shiryen gasar Olympics ta birnin Beijing
2022-01-06 10:54:07 CRI
Yanzu haka dukkanin masu ruwa da tsaki a shirya gasar Olympics ta hunturu da za a bude a birnin Beijing na dukufa wajen tabbatar da nasarar gasar. A iya cewa an kallama dukkanin matakai na wajibi.
An yi nisa wajen yayata wannan gasa
A shekarar nan ta 2021, an zafafa shirye shiryen gudanar da wannan gasa ta birnin Beijing cikin himma da kwazo, an yi nisa sosai wajen shiri, an kuma cimma nasarori masu tarin yawa a wannan bangare. A bana, an yi aiki mai tarin yawa, an gaggauta, kuma sakamakon ya haifar da nasara.
A watan Janairun 2021, aka kammala dukkanin wuraren da za a gudanar da wannan gasa dake birnin Beijing, da wuraren gudanar da ajin nakasassu na gasar baki daya. Tun bayan cimma nasarar samun izini na karbar bakuncin gasar hunturu ta birnin Beijing a shekarar 2015, dubun dubatar masu ayyukan gine gine suka fara aiwatar da sassan ayyukan da aka basu cikin nasara.
Daga watan Fabarairu zuwa Afirilu kuwa, an yi amfani da damar saukar kankara ta karshe gabanin gasar dake tafe, inda a birnin Beijing da Zhangzhakou, aka akaddamar da gwaje gwajen da suka kamata, don gano ko akwai wasu kura kurai, tare da samun kwarewa game da yanayin yadda gasar za ta gudana a zahiri. Kammala wadannan gwaje gwaje cikin himma da kwarewa cikin lokaci takaitacce, ya zama gwajin farko na tabbatar da nasarar gasar Olympics ta huturu ta birnin Beijing musamman a shekarun baya bayan nan.
A watan Yuli, yayin taron kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa karo na 138, gabanin bude gasar Olympics ta birnin Tokyo, kwamitin shirya gasar Olympics na birnin Beijing, ya gabatar da tsare tsaren karshe na shirin sa game da shirya gasar dake tafe, lamarin da ya samu matukar amincewa, da gamsuwa daga shugaban kwamitin na IOC Thomas Bach. Har ma Mr. Bach ya ake da sako dake cewa "Ina fatan za ku ci gaba da jajircewa."
Yayin gasar Olympics da ta ajin masu bukatar musamman ta birnin Tokyo, kwamitin shirya gasar hunturu ta Olympics ta birnin Beijing, ya tura tawagar manyan jami’ai zuwa Japan, domin nazartar yadda gasar ke gudana. Bayan kammala gasar ta Tokyo, wadda aka kammala irin ta ta farko ana tsaka da fama da cutar COVID-19, sassan duniya sun tara karfin su, tare da maida hankali ga gasar dake tafe a Beijing.
Tun daga watan Oktoba, mashirya gasar Olympics ta birnin Beijing suka fara gudanar da babban aikin gwaji na musamman gabanin bude gasar. Sabanin gwajin da aka yi a baya, a wannan karo "an gwada kusan dukkanin kaya da sassan wurare", an aiwatar da gasa da daidaikun hukumomin shirya gasannin kasa da kasa na wasannin hunturu suka shirya.
Yayin wannan gwaji, sama da ‘yan wasa 2,000, da jami’an hukumomi, da jami’an tsare tsare daga kasashen waje sun zo kasar Sin a lokuta mabanbanta. An yi gwajin samar da abinci, da tufafi, da muhallin saukar mutane, da wuraren samun horon wasanni, da ba da kyautuka, da gudanar da zantawar manema labarai, da ayyukan kandagarkin yaduwar cuta da shawo kan ta, da duba kayan da za a yi amfani da su, da gwajin yin amfani da kayan, da atisayen ba da umarni, dukkanin wadannan an yi su a zahiri.
A watan Nuwamba kuma, karkashin tsarin gwajin gasar a matakin kasa da kasa, an fitar da sakamakon tsarin gudanarwa, da tabbaci wajen ba da hidima, an kuma fara ganin nasarar aiki da wuraren gasar. Jagororin hukumomin kasa da kasa na wasanni, da manyan ‘yan wasan motsa jiki na kasa da kasa sun jinjinawa birnin Beijing.
A halin yanzu, an rika an kammala gwajin gasanni a biranen Beijing da Yanqing, kuma an kusa kallama wadanda aka yi a Zhangjiakou. An kuma shirya gudanar da horon mako guda na wasan Biathlon tsakanin ranekun 28 zuwa 31 ga watan Disambar nan. Ana iya cewa, an shafe dukkanin kwanaki ana shirya gasar nan ta Olympics ta birnin Beijing dake tafe.
Bayan da aka yi gwaje gwajen gasar a kauyukan Olympic a manyan wuraren gudanar da gasar guda 3, sauran manyan wuraren da ba na wasanni ba dake birnin Beijing, wadanda za su samar da karin hidimomi su ma sun kammala. Ana sa ran irin wadannan wurare za su samarwa baki hidimomi masu nagarta.
Gina kasaitacciyar gasa cikin farin ciki
Wasannin gasar Olympic sun wuce batun yin takarar lashe lambobi kadai, domin kuwa ana kallon su a matsayin wata al’ada, da dabi’un ta ke ci gaba da wanzuwa cikin tsawon shekaru. A saukake, har kullum gasar hunturu ta Olympics ba ta rabuwa da jan hankalin duniya, da tarayya tare da yin komai tare tsakanin al’ummun kasashe da yankuna daban daban.
Akwai fitila, akwai haske. A ranar 4 ga watan Fabarairu, aka fara gudanar da shagulgulan bude gasar Olympics ta hunturu ta birnin Beijing, a lokacin aka fitar da wutar yula ta gasar mai kunshe da ajin nakasassu.
A ranar 18 ga watan Satumba kuma, aka akarbi wutar yula ta gasar Olympics ta birnin Beijing, daga wurin kunna ta. A ranar 19 ga watan, kwamitin shirya gasar Olympic na kasar Girka, ya mikawa kwamitin shirya gasar na birnin Beijing wannan wuta, wadda ta iso birnin Beijing kwana guda bayan hakan. An tsara kewayawa da wutar, karkashin manufar yayata gasar, da nuna kirkire kirkire, da damawa da sauran al’umma a hukumance. Tsarin ya hada da nuna wasannin wuta da kuma nune nunen gargajiya.
Tsakanin ranekun 2 zuwa 4 ga watan Fabarairun shekarar 2022 dake tafe, za a kewaya da wutar wurare 3 da za a gudanar da gasar ta birnin Beijing. Ana sa ran nuna wasu alamu na wasannin kankara, da dusar kankara masu nasaba da wasannin da za a gudanar, da ma ita kan ta gasar ta Olympic mai tarihi a birnin Beijing, da kuma Yanqing da Zhangjiakou, inda su ma a can za a gudanar da wasu wasanni. A hannu guda kuma, za a nuna abubuwa na ainihi, da tarihi, da fasahohin al’umma da sabbin fasahohin zamani.
Shawo kan kalubale cikin ruwa sanyi
Kandagarki da shawo kan annoba, na ci gaba da zama babban kalubale ga masu karbar bakuncin Olympic, amma gasar Olympics ta birnin Beijing na tunkarar wannan kalubale cikin nutsuwa.
A karshen watan Satumba, babban kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa, ya yi taro, tare da tattauna muhimman manufofi na kandagarki da shawo kan annoba yayin gudanar gasar Olympics ta hunturu ta birnin Beijing, da ajin gasar na nakasassu, inda aka tanadi tsare tsare muhimmai, kamar su rigakafi, lura da dukkanin sassan gasar, da samar da tikiti, da rajistar baki, da wuraren saukar baki, da ayyukan gwajin cutar.
Sin ta gayyaci kowa. Kuma yayin da wannan gasa ta Olympics ta birnin Beijing ke karatowa, ‘yan siyasa da jami’an kwamitin shirya gasar daga Austria, da Faransa, da Cyprus, da Finland, da Girka, da Hungary, da Italiya, da Netherlands, da Sifaniya, da Switzerland, da Rasha, da Belarus sun bayyana cewa, za su shiga a dama da su wajen gudanar da gasar ta Olympics ta birnin Beijing.
Kasashe da dama sun yi magana ta hanyoyi daban daban, da nufin siyasantar da wannan gasa ta Olympics, da siyasantar da wasanni. To sai dai kuma an yi imanin cewa, gasar Olympics ta birnin Beijing dake tafe, za ta hade kan al’ummu daga kasashe da yankuna daban daban, tare da yayata zaman lafiya da ci gaba a duniya. A nata bangare, kasar Venezuela ta fitar da sanarwar gwamnati, dake neman Amurka ta gaggauta dakatar da siyasantar da batun wasanni.
Shi ma kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha Zakharova, ya ce domin cimma bukatun kashin kai, Amurka ta dauki matakan gurgunta tsarin gasar kasa da kasa, tare da kokarin ayyana wasa sabuwar doka game da wasannin kasa da kasa bisa tunani irin na ta.
A yanzu haka, shirye shiryen gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing sun yi nisa. Nan da kusan kwanaki 40, za a gudanar da babban bikin bude wannan gasa, inda al’ummun duniya za su hallara a birni mai tarihin karbar bakuncin gasannin Olympics guda 2!