logo

HAUSA

Wang Wenbin: Rangadin da shugaban kasar Sin ya yi a sassan shirya gasar Olympic na nuni ga muhimman batutuwa 3

2022-01-06 20:18:20 CRI

Wang Wenbin: Rangadin da shugaban kasar Sin ya yi a sassan shirya gasar Olympic na nuni ga muhimman batutuwa 3_fororder_633b20c85a1243ccbb9400c015d48f0b

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce a cikin sakon taya murnar sabuwar shekara da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya bayyana aniyarsa ta sadaukar da wannan gasar Olympic ga daukacin duniya. Kaza lika a ranar farko ta aiki a sabuwar shekarar nan, shugaban na Sin ya ziyarci wuraren da ake shirin karbar bakuncin wannan muhimmiyar gasa ta hunturu, da ajin gasar na nakasassu, hakan na nuni ga muhimman batutuwa guda uku.

Wadannan batutuwa dai sun hada da irin muhimmanci da Sin ke dorawa ga shirya gasar ta Olympic bisa alkawarin da ta riga ta dauka. Na biyu kuma, hakan na nuna yadda Sin din ta shirya tsaf, domin gudanar da gasa mai kayatarwa. Kana na uku Sin na da karfin gwiwar gudanar da wannan gasa bisa cikakken tsaron lafiyar mahalartanta duk da kalubalen annobar Covid-19 da ake fuskanta.  

Wang Wenbin, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na yau Alhamis 6 ga wata. (Saminu)