logo

HAUSA

Shugaban Kongo ya yi kira da a rika samar da rigakafin COVID-19 a Afirka

2022-01-05 09:34:05 CRI

Shugaban Kongo ya yi kira da a rika samar da rigakafin COVID-19 a Afirka_fororder_220105-yaya-Congo

Shugaban Jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso, ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafa wa Afirka ta yadda za su rika samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a cikin kasashensu.

Shugaban na Kongo ya yi wannan kiran ne, yayin bikin taron ganawa da jami'an diflomasiyya da ke kasar. Ya ce, domin jin dadin dukkan bil-adama, ya kamata kasashen duniya su taimakawa Afirka, ba wai kawai wajen samun alluran rigakafi ba, har ma su rika samar da rigakafin a nahiyar. 

Ya ce, bullar nau’in COVID-19 na Omicron na baya-bayan nan, ya kara nuna rashin tabbas game da ganin bayan wannan annoba, tare da sanya wasu kasashe daukar matakin rufe iyakokinsu na wucin gadi.

A karshen watan Disambar 2021 ne, aka kebe shugaban na Kongo, bayan da gwaji ya nuna ba ya dauke da cutar, saboda ya gana da wasu mambobin tawagarsa wadanda suka kamu da COVID-19. (Ibrahim Yaya)