logo

HAUSA

Muhimman abubuwan da Shugaban kasar Sin ya tabo a jawabinsa na murnar sabuwar shekara ta 2022

2022-01-05 09:15:34 CRI

Kamar yadda ya saba gabatar da muhimmin jawabin gasuwar shiga sabuwar a jajeberin kowa ce sabuwar shekara, a bana ma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da irin wannan jawabi na murnar shuiga sabuwar shekarar 2022, ta babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da kuma yanar gizo. Shugaba Xi ya ce shekarar 2021 da muka yi bankwan da ita, tana da ma’ana ta musamman, saboda mun ga yadda wasu abubuwa masu ma’ana da suka faru a tarihin kasar Sin, da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai mulkin kasar. Ya ce, yanzu haka muna kokarin cimma burinmu na gina al’umma mai walwala, da raya kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu, mun kuma kama hanyar cimma dukkan burikanmu na raya kasa, don tababtar da ci gaban al’umma.

Muhimman abubuwan da Shugaban kasar Sin ya tabo a jawabinsa na murnar sabuwar shekara ta 2022_fororder_220105世界22001-hoto4

Xi ya bayyana yadda, Sinawa ke kokarin hidima a cikin gonaki, da kamfanoni, da ungwanni, da makarantu, da asibitoci, da sansanonin soja, da cibiyoyin nazarin kimiya da fasaha. A kokarin samar da gudunmawa, da cimma dimbin nasarori, a wannan shekara mun ga yadda kasar Sin take kara samun ci gaba, ta hanyar jajircewa. Jama’ar kasar suna da kokari. Ana ta samun ci gaban harkoki a fannoni daban daban. Kana ana kokarin gadon fasahohi na wasu sana’o’i.

Muhimman abubuwan da Shugaban kasar Sin ya tabo a jawabinsa na murnar sabuwar shekara ta 2022_fororder_220105世界22001-hoto3

Sauran fannonin da shugaban ya tabo, sun hada da, yadda aka shirya gagarumin bikin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, inda aka yi bitar wasu daga cikin nasarorin da aka cimma cikin wadannan shekaru 100, da ci gaban da aka samu a yakunan HK da Macao, shirin karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da yadda yan sama jannatin kasar Sin ke gudanar da aikin kafa tashar binciken sararin samniyar kasar, da yadda jamian diflomasiyar kasar da maaikatan kamfanoni da daidaikun sinawa ke aiki a ketare da sauransu. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya da dukkan alheran dake cikin shekarar 2022. Amin. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)