logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Kyrgyzstan sun taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya

2022-01-05 11:02:51 CRI

Shugabannin Sin da Kyrgyzstan sun taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya_fororder_220105-yaya-Kyrgyz

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kyrgyzstan, Sadyr Zhaparov, suka yi musanyar taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Xi ya ce, bunkasuwar dangantakar Sin da Kyrgyzstan, ba wai kawai ta amfanar da kasashen biyu da jama'arsu ba, har ma tana taimakawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tsakiyar Asiya.

Ya kuma ba da shawarar cewa, bangarorin biyu su yi amfani da bikin cika shekaru 30 din, a matsayin wani sabon mafari, don kara amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da zurfafa hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya, da daga matsayin alakar dake tsakanin Sin da Kyrgyzstan bisa manyan tsare-tsare zuwa sabbin matakai.

A cikin nasa sakon, shugaba Zhaparov ya ce, a shirye yake ya yi aiki tare da kasar Sin, don kara zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)