logo

HAUSA

Ya Kamata Amurka Ta Sauya Tunaninta Kan Kasar Sin A Shekarar 2022

2022-01-05 16:51:51 cri

Ya Kamata Amurka Ta Sauya Tunaninta Kan Kasar Sin A Shekarar 2022_fororder_11

A shekarar 2021 da muka yi bankwana da ita, duniya ta kalli yadda kasashen yammacin duniya, musamman Amurka ta rika tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da sunan wai kare hakkin bil-Adama ko salon demokiradiya, matakin da ya saba dokoki da ma huldar kasa da kasa.

Bugu da kari, a shekarar 2021, duniya ta ga yunkuri na wani salo na yaki da Amurka ta yi amfani da shi kan kasar Sin, wanda ta shafe shekaru da dama tana yi, lamarin da ya karu cikin 'yan shekarun da suka gabata. Kama daga neman durkusar da kamfanoninta na fasahar kere-kere, da kamfanin sadarwa na Huawei da daidaikun Sinawa babu gaira babu dalili, zuwa fara yakin ciniki da fasahar kere-kere. Daga tsoma baki a batun tekun kudancin kasar Sin, da sunan 'yancin zirga-zirga zuwa yada jita-jita game da batun da ya shafi hakkin dan Adam a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da kuma yankin Tibet mai cin gashin kansa dukkansu na kasar Sin.

Haka kuma kasar Amurka ta tsara wasu dabarun yaki daya bayan daya, a wani yunkuri na ta da zaune tsaye a kasar Sin, da kassara ci gabanta, da ma tasirinta a harkokin kasa da kasa, sai dai dukkan wadannan makarkashiya ba su kai ga cimma nasara ba.

Yayin da irin wadannan yake-yake masu yawa da Amurka ta tayar take ganin sun taimaka mata wajen ganin bayan abokan hamayyarta, a hannun guda kuma, suna lalata tushen mulkin danniya na Amurkar. Domin duk fa'idar da Amurka ta girba na gajeren lokaci, haka nan kuma take yiwa kanta illa na dogon lokaci.

Masu fashin baki na fatan, yayin da muka shiga sabuwar shekara ta 2022, shekarar da al’ummar duniya ke fatan ganin bayan annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya, gami da kalubabalolin da wannan annoba ta haifar ga daukacin rayuwar bil-Adama, da kulla alakar samun nasara tare. Da fatan ita ma Amurka da kawayenta za su sauya tunaninsu game da kasar Sin, su hada kai da ita, ta yadda duniya baki daya za ta amfana, maimakon yin fito na fito da ba zai amfani kasashen biyu da al’ummominsu da ma duniya baki daya ba.