logo

HAUSA

DPRK ta harba wasu rokoki da ba a tantance su ba a tekun gabashin yankin

2022-01-05 11:10:16 CRI

DPRK ta harba wasu rokoki da ba a tantance su ba a tekun gabashin yankin_fororder_220105-ahmad-DPRK

Koriya ta arewa (DPRK) ta harba wasu makamai masu linzami da ba a tantance su ba zuwa tekun gabashin yankin, tawagar dakarun tsaron hadin gwiwar Koriya ta kudu (JCS), ta bayyana hakan a yau Laraba.

A cewar sanarwar da JCS ta fitar, DPRK ta harba makaman rokar ne ba tare da yin wani karin haske ba.

Wannan shi ne karon farko da Koriya ta arewan ta yi gwajin makamai masu linzami a shekarar 2022. Gwaji na baya bayan nan da ta gudanar shi ne na ranar 19 ga watan Oktoban bara a lokacin da DPRK ta yi gwajin sabon samfurin makami mai linzami dake gudu a tsakiyar teku. (Ahmad)