logo

HAUSA

Jagoran mulkin Sudan ya ce kofa a bude take don tattaunawar daidaita rikicin siyasar kasar

2022-01-05 10:14:00 CRI

Jagoran mulkin Sudan ya ce kofa a bude take don tattaunawar daidaita rikicin siyasar kasar_fororder_220105-ahmad-Sudan

Shugaban majalisar mulkin kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya bayyana a ranar Talata cewa, kofa a bude take ga dukkan bangarorin siyasar kasar domin tattauna yadda za a kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke ci gaba da fuskanta.

Majalisar mulkin kasar ta sanar da cewa, Al-Burhan ya yi wannan tsokaci ne a ofishinsa a ranar Talata a yayin ganawa da Brian Shukan, babban jami’in diflomasiyyar kasar Amurka dake Khartoum.

Ya kuma jaddada bukatar ci gaba da tattaunawar a tsakanin dukkan bangarorin kasar da nufin cimma matsaya game da yadda za a daidaita wa’adin gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Al-Burhan ya ce, kofofi za su ci gaba da kasancewa a bude ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki a siyasar kasar, da matasan dake yin bore, domin a cimma yarjejeniyar kammala tsare-tsaren kafa shugabancin rikon kwarya wanda zai share fagen kafa tsarin demokaradiyya ta yadda za a samu sahihin sakamakon zabe wanda zai tabbatar da kafuwar gwamnatin farar hula wacce za ta biya cikakkun muradun al’ummar Sudan. (Ahmad)