logo

HAUSA

Kasar Sin ta dade da kokarin kawar da makaman nukiliya daga fadin duniya

2022-01-05 21:28:15 CRI

Kasar Sin ta dade da kokarin kawar da makaman nukiliya daga fadin duniya_fororder_1

Tun farkon bana, shugabannin wasu manyan kasashe biyar dake mallakar makaman nukiliya, ciki har da Sin, da Rasha, da Amurka, da Birtaniya gami da Faransa, sun fitar da wata sanarwa cikin hadin-gwiwa, mai taken “hadaddiyar sanarwa dangane da hana yakin nukiliya, da kaucewa yin takarar makaman soja”, inda suka jaddada cewa, babu wata kasa da za ta iya samun nasara a yakin makaman nukiliya, kana bai dace a yi irin wannan yaki ba, kuma ba za su yi amfani da makaman nukiliyarsu kan juna ko sauran kasashe ba, kuma burinsu na karshe shi ne, gina duniya ba tare da makaman nukiliya ba, bisa tushen tabbatar da tsaron kowace kasa.

Raya makaman nukiliyar da kasar Sin ta yi, wani zabi ne da aka tilastawa kasar ta yi, a wani lokaci na musamman don tinkarar kalubale, da hana barkewar yakin nukiliya. Tun da ta fara mallakar makaman, ya zuwa yanzu, kasar ta Sin ta dade da kira da a haramta, gami da lalata dukkanin makaman nukiliya, kana ta yi alkawarin cewa, ba za ta yi amfani da makaman ba kan kasashe da yankunan da ba su da makaman nukiliya, ba tare da wani sharadi ba, kuma ita ce kasa daya kadai da ta yi irin wannan alkawarin daga cikin wadannan kasashe biyar.

Abun lura a nan shi ne, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da tsaro a duniya, yana bukatar kokarin dukkan kasashen biyar dake mallakar makaman nukiliya, musamman ita Amurka da ta fi karfin tattalin arziki, ya kamata ta dauki matakai a zahiri.

Amma a shekarar da ta gabata, Amurka ta yi yunkurin haifar da barazanar nukiliya, al’amarin da ya sa ta zama babban hadari ga bangaren tsaron nukiliya na duniya. Bayan da aka rattaba hannu kan sanarwar a wannan karo, ya dace Amurka ta cika alkawarin da ta yi tare da daukar matakan zahiri.  (Murtala Zhang)