logo

HAUSA

Waiwaye Adon Tafiya

2022-01-04 15:59:27 CRI

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_1

Shekarar 2021 da muka yi ban kwana da ita, shekara ce mai matukar muhimmanci ga dangantakar kasar Sin da kasashen Afirka. Ganin yadda cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba da addabar kasa da kasa, gami da manyan sauye-sauyen da aka samu a duk fadin duniya baki daya, kasar Sin da kasashen Afirka sun kara marawa juna baya, da samar da ci gaba kafada da kafada, al’amarin da ya sa aka samu muhimman nasarori da dama wajen yaki da annobar, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman ci gaba.

A shekara ta 2021, wadda ita ce ta cika shekaru 65 da fara kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, manyan shugabanni da jami’an gwamnatocin kasashen bangarorin biyu, sun ci gaba da yin mu’amala da shawarwari tsakaninsu, don kara ciyar da alakokinsu gaba. A farkon shekarar 2021, ministan harkokin wajen Sin Mista Wang Yi ya ziyarci wasu kasashen Afirka biyar, ciki har da Najeriya, da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, da Botswana, da Tanzaniya da kuma Seychelles, al’amarin da ya kasance muhimmiyar al’adar kasar Sin, wato ministan harkokin wajen kasar ya kan ziyarci Afirka a farkon kowace shekara. Sa’an nan a tsakiyar shekarar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi shawarwari tare da takwarorinsa na wasu kasashen Afirka da dama, ta hanyar buga waya ko aikawa da sako, ciki har da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, da Saliyo, da Jamhuriyar Kongo da Tanzaniya da Malawi da kuma Rwanda. A karshen shekarar ma, an yi nasarar gudanar da taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC a birnin Dakar na kasar Senegal, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, inda shugaba Xi ya gabatar da wani muhimmin jawabi ta kafar bidiyo, mai taken “Sa himma da inganta hadin-gwiwa don a gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka a sabon zamaninmu”. Shugaba Xi ya bayyanawa duniya wasu manyan ayyuka tara, da za’a gudanar don inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka a shekaru uku masu zuwa, da ma a cikin wani dogon lokaci fiye da haka, wadanda suka shafi kiwon lafiya, da rage talauci, da raya kasuwanci, da kara zuba jari, da bunkasa harkokin sadarwar zamani, da kiyaye muhallin halittu, da inganta kwarewa, da kara musanyar al’adu, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da dai sauran makamantansu, al’amarin da ya kafa sabuwar alkibla ga ci gaban huldodin Sin da Afirka.

Kamar yadda shugaba Macky Sall na kasar Senegal wadda ta karbi bakuncin taron dandalin FOCAC a shekara ta 2021 ya ce, har kullum kasar Sin tana mutunta ’yanci da cikakken mulkin kai gami da al’adu na kasashen Afirka, da nuna musu goyon-baya wajen samar da ci gaba, kana kasar Sin tana tsayawa kan ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duk duniya, a wani kokari na kare muradin ci gaban kasashe masu tasowa.

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_2

Idan mun dubi muhimman abubuwan da suka wakana a shekara ta 2021 ta fuskar dangantakar Sin da Afirka, yaki da annobar COVID-19 cikin hadin-gwiwa da raya tattalin arziki sun fi jawo hankali.

Har kullum kasar Sin tana tare da kasashen Afirka wajen yakar cutar mashako ta COVID-19, inda take kira a tabbatar da adalcin raba alluran riga-kafin cutar, musamman ga kasashen Afirka. Ya zuwa shekara ta 2021, adadin alluran da kasar Sin ta samarwa Afirka wajen yakar cutar ya zarce miliyan 200, kuma domin taimakawa kungiyar tarayyar Afirka wato AU cimma burin sanya alluran riga-kafin cutar ga kaso 60 bisa dari na al’ummomin Afirka, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, a shekara ta 2022, kasarsa za ta kara samarwa Afirka alluran riga-kafin da yawansu ya kai biliyan 1, ciki har da miliyan 600 a matsayin kyauta. Har wa yau kuma, tun farkon farawa, kasar Sin ta hada kai tare da kasashen Afirka domin samar da alluran. A watan Yulin shekara ta 2021, kasar Masar ta kammala aikin samar da alluran riga-kafin mai suna SINOVAC na kamfanin kasar Sin, abun da ya shaida cewa, kasar Sin ta dauki matakai a zahiri, domin karfafa hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka ta fannin yaki da cutar COVID-19.

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_3

Baya ga yaki da cutar COVID-19 cikin hadin-gwiwa, samar da ci gaba, da farfado da tattalin arziki kafada da kafada, wani muhimmin abu ne na daban a alakar Sin da Afirka. A shekara ta 2021, Sin da Afirka sun ci gaba da karfafa hadin-gwiwa da mu’amala a fannoni daban-daban, don neman farfado da tattalin arziki, da kyautata rayuwar al’umma, musamman a fannonin da suka shafi inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da harkar lafiya, da bada ilimi, da daukar ma’aikata, da ayyukan gona, da harkar hako ma’adinai, da sana’ar kere-kere, da kasuwanci, da zuba jari, da sadarwar zamani, da jigilar kayayyaki, da sabbin makamashi da sauransu. Idan mun dauki bangaren gina muhimman ababen more rayuwar al’umma a matsayin misali, a shekara ta 2021, muhimman ayyukan hadin-gwiwar Sin da Afirka na da dimbin yawa, kamar su tashar ajiye manyan kwantenoni dake Sokhna na kasar Masar, da tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa dake Souapiti na kasar Guinea, da layin dogon da ya hada Legas da Ibadan, gami da tagwayen hanyoyin zamani da aka gina a birnin Maidugurin jihar Borno a tarayyar Najeriya, da babbar hanyar mota dake hada Yaoundé da Bafoussam a kasar Kamaru, gami da wasu filayen saukar jiragen sama da aka gina a kasashen Zambiya da Mozambique da sauransu. Ainihin dalilin da ya sa kasar Sin take kokarin taimakawa kasashen Afirka inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma shi ne, domin samar da dauwamammen ci gaba ga nahiyar.

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_4

Amma wasu kasashen yammacin duniya, sun dade da shafawa kasar Sin bakin fenti, inda suka ce wai kasar Sin ta tsunduma kasashen Afirka cikin matsalar basussuka, ciki har da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. A yayin ziyararsa tarayyar Najeriya a watan Nuwambar 2021, Blinken ya zargi kasar Sin da haifar da matsalar basussuka ga kasashen Afirka. Amma nan da nan, furucinsa ya jawo suka daga wajen ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, inda ya ce, basussukan da Najeriya ta ci, ba su da yawa, wadanda Najeriya ke iya biya ne, kuma dalilin da ya sa aka zabi kamfanonin kasar Sin wajen bunkasa manyan ababen more rayuwa a kasar shi ne, kamfanonin sun kware, kana suna samar da farashi mai sauki. Mista Onyeama ya kuma jaddada cewa, “ciniki mafi kyau muke magana, a maimakon zancen wannan kasa ko waccan kasa.”

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_5

Can ma a kasar Uganda, akwai wasu kafafen yada labaran kasashen yamma wadanda suka ce, wai kasar Sin da Uganda sun daddale wata yarjejeniya, inda Sin ta gindaya sharadin cewa, idan Uganda ba ta iya biyan bashin da kasar Sin ta ba ta ba, Sin za ta karbe iko da filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Uganda wato Entebbe International Airport. Sai dai kuma shugaban Uganda Yoweri Museveni ya fito fili don musunta wannan labarin, inda a cewarsa, kasar Sin ta fi kasashen yammacin duniya nuna sha’awa da kwazo wajen zuba jari a Uganda, kuma ta ga damammakin ciniki, shi ya sa ta zo yin kasuwanci tare da Uganda. Museveni ya kuma jaddada cewa, kasarsa za ta biya bashi da kudi, maganar biyan bashi da filin jiragen sama tamkar abun dariya ne kuma jita-jita ne kawai.

Dadin dadawa kuma, kasar Sin ta kara bullo da wasu muhimman shawarwari a Majalisar Dinkin Duniya a bara, domin taimakawa kasashen Afirka tinkarar kalubalen cutar COVID-19, da lalibo hanyoyin daidaita matsalolinsu masu dacewa. Kana, kasar Sin ta ki yarda da wasu kasashen yammacin duniya su yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka, saboda al’ummar Afirka su ne kashin baya wajen daidaita matsalolin kasashensu. Su ma kasashen Afirka har kullum suna ta marawa muradun kasar Sin baya, musamman kan batutuwan da suka jibanci yankunan Taiwan, da Xinjiang, da Hong Kong, da batun hakkin dan Adam, al’amarin da ya kara inganta alakokin Sin da Afirka, da taimakawa sosai wajen gina al’ummomin bangarorin biyu masu kyakkyawar makoma ta bai daya.

Waiwaye Adon Tafiya_fororder_6

Hausawa kan ce, waiwaye adon tafiya. Takaita nasarorin hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka a shekara ta 2021, shi ne dalilin kara kyautata dangantakarsu a sabuwar shekarar da muke ciki wato 2022. Yadda za’a yi domin kawar da talauci, da samar da ci gaba mai dorewa, muhimmin aiki ne dake gaban kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka. Haka kuma, annobar COVID-19 na ci gaba da haifar da illa ga kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki, da rayuwar dan Adam. Kasar Sin tana son bayyanawa nahiyar Afirka sirrinta na samun nasarar yaki da talauci, da kyautata rayuwar al’umma, gami da taka birki ga yaduwar cutar COVID-19, kuma akwai kwararru da masanan Afirka da dama, wadanda suka bayyana aniyarsu ta samar da ci gaba tare da kasar Sin. Olalekan A. Babatunde, manazarci ne dake aiki a cibiyar binciken zaman lafiya da magance tashin hankali a tarayyar Najeriya, ya kuma wallafa wani sharhin kwanan baya dake cewa, ya dace Najeriya ta maida hankali sosai kan damammakin da aka bayar sakamakon bunkasa dangantaka da kasar Sin, musamman a fannin kyautata rayuwar al’umma. Shi ma a nasa bangaren, Osidipe Adekunle, dan Najeriya dake aiki a cibiyar nazarin harkokin Afirka a jami’ar horas da malamai ta Zhejiang a kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Sin tana bakin kokarinta, wajen rage gibin dake tsakanin masu arziki da masu fama da talauci, da taimakawa marasa galihu samun kudin shiga, al’amarin da ya zama babban darasi ga kasashe masu tasowa, musamman kasashen dake nahiyar Afirka.

A sabuwar shekara ta 2022, ya dace kasar Sin da kasashen Afirka su ci gaba da marawa juna baya, da samar da ci gaba mai inganci cikin hadin-gwiwa, da kara gina al’ummomin bangarorin biyu, masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)