logo

HAUSA

Wang Wenbin: Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen ingiza jagorancin duniya a fannin nukiliya

2022-01-04 21:06:42 CRI

Wang Wenbin: Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen ingiza jagorancin duniya a fannin nukiliya_fororder_309c236f8c3b233e7b5d57

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce tun fil azal, kasar Sin na nacewa manufar kyautata tsaron nukiliya domin kare kai, tana kuma aiwatar da manufofi na tabbatar da ba ta fara amfani da makaman nukiliya a kan wani bangare ba. Kaza lika tana kayyade makaman nukiliyarta daidai da bukatar tsaron kasa.

Wang Wenbin, ya ce wadannan matakai na taka rawar gani, wajen samar da daidaito tsakanin kasa da kasa a fannin. Har ila yau, Sin za ta ci gaba da raba basirar ta, da dabarun ingiza jagorancin duniya a fannin nukiliya, kuma za ta ci gaba, da yin hadin gwiwa da dukkanin kasashen dake fatan wanzar da zaman lafiya a duniya.

Wang wanda ya yi wannan tsokaci, yayin taron ‘yan jaridu na Talatar nan, ya amsa wata tambaya da aka yi masa, game da batun sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa, mai nasaba da dakile yakin makaman nukiliya, da kaucewa rige rigen mallakar makamai da kasashe 5 suka sanyawa hannu, inda ya ce a jiya Litinin 3 ga wata, shugabannin kasashe 5 da suka mallaki makaman nukiliya, wato Sin, da Rasha, da Amurka, da Birtaniya da Faransa, sun fitar da sanarwar bai daya, wadda ta dada tabbatar da cewa, ba wata kasa da za ta hari wata da makaman nukiliya a tsakanin su, ko ma wata kasar ta daban. Sun kuma yi alkawarin martaba yarjeniyoyi da aka kulla, tsakanin kasashe biyu biyu, da ma na kasa da kasa masu nasaba da dakile mallakar makamai, inda suka amince ba za su yi fito na fito na soji da juna ba, kuma za su kaucewa matakan rige rigen mallakar makamai.  (Saminu)