logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya kai ziyara ta farko a sabuwar shekara a nahiyar Afirka

2022-01-04 14:04:06 CRI

Ministan harkokin wajen Sin ya kai ziyara ta farko a sabuwar shekara a nahiyar Afirka_fororder_0104-1

Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai kai ziyara a kasashen Eritrea, da Kenya da kuma Comores tun daga ranar 4 zuwa 7 ga wannan wata bisa gayyatar da aka yi masa. Kamar yadda aka saba, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kiyaye al’adar fara kai ziyara kasashen Afirka a kowa ce sabuwar shekara har tsawon shekaru 32.

Wakiliyar musamman ta gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Xu Jinghu ta bayyana cewa, duk da yanayin tinkarar nau’in Omicron na cutar COVID-19, Sin ta kiyaye al’adar fara kai ziyara nahiyar Afirka a farkon kowa ce sabuwar shekara, wannan ya shaida cewa, Sin da Afirka suna kiyaye zumunci mai karfi tamkar ‘yan uwa. Ta ce,“Ba kwatsam ba ne ziyarar farko da kasar Sin take kaiwa nahiyar Afirka a kowace shekara har tsawon shekaru 32 a jere, wannan wani shiri ne na sada zumunta na musamman da kasar Sin ta zaba kuma ta tsara shi. Karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, wani zabi ne bisa manyan tsare-tsare na manufofin harkokin wajen kasar Sin. Duk da sauye-sauyen yanayi da duniya ke fuskanta, wannan al’adar nan ba zata taba sauya ba.”

Xu Jinghu ta bayyana cewa, manufar ziyarar Wang Yi a Afirka a wannan karo, ita ce sa kaimi ga aiwatar da sakamakon da aka cimma a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da zurfafa dangantakar abokantaka da kasashen Afirka, da sabbin matakan hadin gwiwa, da nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, da farfado da tattalin arziki, hakan ya shaida cewa, Sin tana kokarin cika alkawarinta. (Zainab)