Gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu a Beijing za ta nunawa duniya karfin hadin-gwiwa
2022-01-04 20:52:30 CRI
Nan da wata daya za’a kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin sanyi a birnin Beijing na kasar Sin, inda kasa da kasa ke sa ran ganin wata gagarumar gasa, da fatan za’a kawar da sabanin ra’ayi, da zama tsintsiya madaurinki daya, don inganta hadin-gwiwar al’ummomin kasashe daban-daban, duk da ci gaban yaduwar cutar COVID-19.
A halin yanzu, kasa da kasa na kara kira da a habaka hadin-gwiwa, da kin yarda da saka batun siyasa cikin wasannin motsa jiki. Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, Mista Thomas Bach, ya wallafa wani sharhi kwanan nan, inda ya nuna cewa, gasar Olympics ta lokacin hunturu da za ta gudana a Beijing, za ta kasance wani muhimmin lokaci, inda duk duniya za ta hadu bisa ra’ayin sada zumunta da inganta hadin-gwiwa.
Birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wanda ya taba karbar bakuncin gasar Olympics na lokacin zafi, kuma zai shirya gasar a lokacin sanyi, zai nunawa duk duniya wata kasaitacciyar gasa bisa tattalin kudi, da tsaro da kayatarwa, da bayyana kyawawan halayen Olympics, a wani kokari na karfafa gwiwar duniya don yakar annobar COVID-19. (Murtala Zhang)