logo

HAUSA

Shugaban kasar Mozambik da mai dakinsa sun kamu da cutar COVID-19

2022-01-04 10:30:23 CRI

Shugaban kasar Mozambik da mai dakinsa sun kamu da cutar COVID-19_fororder_220104-Mozambique-Ahmad

Shugaban kasar Mozambik Filipe Nyusi, da mai dakinsa Isaura Nyusi, sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, ofishin dake kula da fadar shugaban kasar ne ya bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar a daren Litinin.

A cewar sanarwar, shugaban kasar da uwar gidansa, dukkansu sun kamu da cutar ne ba tare da nuna alamomin kamuwa ba, an gano suna dauke da cutar ne bayan sakamakon gwajin da aka yi musu da yammacin ranar Litinin ya nuna sun kamu da cutar, kuma a halin yanzu sun killace kansu.

A cewar sanarwar, bisa lura da halin da ake ciki na karin yaduwar annobar COVID-19 nau’in Omicron, ya sa shugaban kasar da mai dakin nasa suka hanzarta yin gwajin, inda sakamakon gwajinsu ya nuna sun kamu da cutar nau’in Omicron.

Bayanai sun nuna shugaban kasar ya gudanar da wasu aikace-aikace da suka hada da ziyartar wurare daban-daban, da halartar tarukan ganawa da wakilai da dama a matakin kasa har ma fiye, a cikin kwanakin karshe na shekarar 2021.

Sanarwar ta ce, domin kiyaye ka’idojin yaki da cutar, duk da cewar ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba, amma shugaban kasa Nyusi da mai dakinsa sun dauki matakin gaggawa na killace kansu, inda suke zaman jiran sakamakon gwajin cutar ta aka yi musu. (Ahmad)