logo

HAUSA

Ziyarar Ministan Wajen Kasar Sin A Afirka Ta Shaida Zumuntar Da Ke Tsakanin Sin Da Afirka

2022-01-04 20:38:07 CRI

 Ziyarar Ministan Wajen Kasar Sin A Afirka Ta Shaida Zumuntar Da Ke Tsakanin Sin Da Afirka_fororder_wang-yi-4

A yau Talata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Mista Wang Yi, ya fara ziyara a wasu kasashen dake nahiyar Afirka, da suka hada da Eritrea, da Kenya, da Comores. Hakan ya kasance wata al’adar da kasar Sin ta kiyaye cikin shekaru 32 da suka gabata, inda a farkon kowace shekara, ministan harkokin wajen kasar ya kan kai ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka.

Idan ba mu manta ba, a farkon shekarar bara, Mista Wang Yi ya ziyarci Najeriya, da Congo Kinshasa, da Botswana, da Tanzania, da Seychelles. Kana a farkon shekarar 2020, ya kai ziyara Masar, da Djibouti, da Burundi, da Zimbabwe, da dai sauransu. Wato ministan wajen kasar Sin ya kan ziyarci mabambantan kasashen dake nahiyar Afirka a shekaru daban daban. Ta haka, ministocin harkokin wajen kasar Sin na baya da na yanzu, sun zagaya duk nahiyar Afirka har sau da dama, cikin shekaru 32 da suka wuce, bayan da suka fara wannan al’ada a shekarar 1991.

Ziyarar Ministan Wajen Kasar Sin A Afirka Ta Shaida Zumuntar Da Ke Tsakanin Sin Da Afirka_fororder_wang-yi-1

Me ya sa suke son zuwa nahiyar Afirka a farkon duk shekara? Amsa ita ce saboda kasar Sin ta dora matukar muhimmanci kan huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka. Manzon musamman mai kula da harkoki masu alaka da kasashen Afirka ta gwamnatin kasar Sin Madam Xu Jinghu, ta taba bayyana cewa, “wata babbar manufar da kasar Sin ta dade tana tsayawa a kai, ita ce kokarin karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka.” Ko da yake nau’in Omicron na cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa cikin sauri a kasashe daban daban, amma wannan yanayi bai hana ministan wajen kasar Sin aiwatar da al’adar ba. Wannan ma ya shaida zumuntar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Tarihi shi ma ya nuna dalilin da ya sa ake samun kauna da kishi tsakanin Sin da Afirka. Saboda kasar Sin da kasashen Afirka suna da tarihi iri daya  na zama karkashin mulkin danniya na ‘yan mulkin mallaka na kasashen dake yammacin duniya, kana suna da buri iri daya na tabbatar da ‘yancin kan kasa, da samun ci gaban tattalin arziki da na al’umma. Don haka suna amincewa da juna. Kasar Sin ta dade tana kokarin taimakawa kasashen Afirka samun damar raya kai, ta wata hanyar da ta dace da yanayinsu, yayin da a nasu bangare, kasashen Afirka suka nuna wa kasar Sin goyon baya, a kokarinta na tabbatar da tsaro, da dinkuwar kasa, da neman damar daukaka matsayin al’ummarta a idanun al’ummun duniya. Ko da yake a kan samu sauyawar yanayin al’amuran duniya, amma Sin da Afirka aminai ne na ko da yaushe.

Ziyarar Ministan Wajen Kasar Sin A Afirka Ta Shaida Zumuntar Da Ke Tsakanin Sin Da Afirka_fororder_wang-yi-2

Ziyarar ministan wajen kasar Sin a Afirka, ta shaida zumunci, baya ga kuma ta haifar da moriya. A watan Janairun bara, Mista Wang Yi, ya kai ziyara a Najeriya da wasu kasashe 4 dake nahiyar Afirka, inda ya yi alkawarin ba da taimako ga kasashen Afirka, ta fuskar dakile annobar COVID-19, da farfado da tattalin arziki. Daga baya, zuwa watan Disamban bara, kasar Sin ta riga ta samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 kimanin miliyan 180 ga kasashen Afirka. Kana ta yi kokarin raba fasahohin dakile cutar tare da aminanta dake Afirka, da kai dauki na kayayyakin da ake bukata, wadanda aka kai su wurare daban daban dake nahiyar Afirka. A sa’i daya, hadin gwiwar bangarorin 2 a fannin tattalin arziki ita ma ta karfafa. Ya zuwa watan Oktoban bara, darajar kayayyakin da kasashen Afirka suka sayar zuwa kasar Sin, ta kai dalar Amurka biliyan 201.1, adadin da ya karu da kashi 37.5% bisa makamancin lokaci na shekarar 2020.

Ziyarar Ministan Wajen Kasar Sin A Afirka Ta Shaida Zumuntar Da Ke Tsakanin Sin Da Afirka

Ban da wannan kuma, ziyarar da Mista Wang Yi ya kaddamar a yau, tana da wata ma’ana ta musamman. Domin a watan Nuwamban bara, an gudanar da taron ministoci na 8 karkashin laimar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, a kasar Senegal, inda aka sanar da wasu manyan ayyuka guda 9 da bangarorin Sin da Afirka za su yi hadin gwiwa a kai. Saboda haka, a wannan ziyarar da yake yi, Mista Wang Yi zai nemi ganin wani yanayi na aiwatar da wadannan ayyuka 9, da cika alkawarin da kasar Sin ta yi na samar da karin alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 1 ga kasashen Afirka, don taimakawa nahiyar cimma burin yi wa kashi 60% na al’ummun kasashen allurar rigakafi cikin shekarar 2022.

Ziyarar da Mista Wang Yi yake yi, wata karfafawa ce mai kyau ga huldar hadin kai ta kasashen Afirka da kasar Sin a shekarar nan ta 2022. Muna sa ran ganin yadda kasar Sin za ta cika alkawari, na karfafa hulda da kasashen Afirka, da samar da karin gudunmowa a fannonin dakile annoba, da farfado da tattalin arziki, da tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a kasashen Afirka. (Bello Wang)