logo

HAUSA

Wadanne fannoni ne suka bayyana sabon ra’ayin samar da ci gaba na kasar Sin?

2022-01-03 15:48:22 CRI

Wadanne fannoni ne suka bayyana sabon ra’ayin samar da ci gaba na kasar Sin?_fororder_1

Shekarar da ta kare wato 2021, shekara ce ta farko da kasar Sin ta kaddamar da babban aikinta na gina kasa wadda za ta zama ta zamani, dake bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni, inda kasar ta shiga wani sabon mataki na neman bunkasuwa.

Tun shekara ta 2021, tabbatar da sabon ra’ayin samar da ci gaba yadda ya kamata, kuma daga dukkanin fannoni, ya zama muhimmin fanni a cikin harkokin mulkin kasa da shugaba Xi Jinping ke tafiyarwa. To ko wadanne fannoni ne suka bayyana irin wannan sabon ra’ayin?

Wadanne fannoni ne suka bayyana sabon ra’ayin samar da ci gaba na kasar Sin?_fororder_2

Na farko shi ne yin kirkire-kirkire. A watan Maris din shekara ta 2021, a yayin ziyarar aikinsa wani kamfanin dake lardin Fujian, shugaba Xi ya jaddada cewa, shirin raya kasar Sin na dogara kan harkokin yin kirkire-kirkire, kuma za’a nuna cikakken goyon baya ga duk wani aikin da zai bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.

Wadanne fannoni ne suka bayyana sabon ra’ayin samar da ci gaba na kasar Sin?_fororder_3

Na biyu, sabon ra’ayin samar da ci gaba, dake maida hankali kan kiyaye muhalli. Sauyin yanayi kalubale ne ga daukacin al’ummar duniya. A yayin taron koli kan batun yanayi da aka gudanar a ranar 22 ga watan Afrilun shekarar 2021, shugaba Xi Jinping ya sanar da aniyar kasarsa, ta kaiwa kololuwar fitar da iskar Carbon Dioxide ya zuwa shekara ta 2030, da kuma samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekara ta 2060. Har wa yau, fadin gandun daji ya zarce kaso 23 bisa dari na fadin duk kasar Sin.

Na uku, sabon ra’ayin samar da ci gaba yana maida hankali kan aikin zamanantar da kasar Sin, inda dan Adam da muhallin halittu za su iya zama cikin jituwa. Kasar Sin za ta ci gaba da aiki tukuru wajen kiyaye muhalli, da kokarin samar da zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu, a wani kokari na gina rayuwar duk duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)