logo

HAUSA

Shugaba Ramaphosa ya sha alwashin bincikar dalilin gobarar da ta shafi ginin majalissar dokokin kasar

2022-01-03 16:07:29 CRI

Shugaba Ramaphosa ya sha alwashin bincikar dalilin gobarar da ta shafi ginin majalissar dokokin kasar_fororder_0824ab18972bd40726f830b7371132580eb309da

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya sha alwashin tabbatar da cikakken bincike, dangane da musabbabin aukuwar gobara, a ginin majalissar dokokin kasar dake birnin Cape Town, yana mai cewa, yana da masaniyar an damke wani, kuma ana masa tambayoyi game da aukuwar lamari.

Wata sanarwa ta ce, an sanar da hukumar kashe gobara tashin wutar da misalin karfe 5:03 na safiya, daga baya aka sauya lokacin zuwa 6:12, kuma ta shafi sassan ginin tsohon zauren majalissar dokokin kasar, mai kunshe da ofisoshin majalissar wakilai, da kuma ginin ‘yan majalissun dattijai na lardunan kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, ‘yan kwana kwana sun kashe wutar da ta tashi a bangaren tsohon ginin, yayin da suke ta kokarin kashe wadda ke cin sabon ginin, ko da yake dai ba wanda ya ji rauni sakamakon tashin gobarar. Kaza lika ba a kai ga tantance musabbabin aukuwar ta ba, sai dai an riga an fara gudanar da bincike. (Saminu)