logo

HAUSA

WHO ta jinjinawa Rwanda saboda nasarorin yiwa al’umma riga-kafin cutar COVID-19

2022-01-03 16:21:51 CRI

WHO ta jinjinawa Rwanda saboda nasarorin yiwa al’umma riga-kafin cutar COVID-19_fororder_1

Bisa sabuwar kididdigar da cibiyiar nazarin likitancin halittu ta kasar Rwanda ta fitar a jiya Lahadi, kawo yanzu an riga an yiwa mutane kusan miliyan 5.5 alluran riga-kafin cutar COVID-19, adadin da ya kai kaso 42 bisa dari na daukacin al’ummar kasar.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ta yi kira ga dukkan kasashe, da su kammala aikin yiwa kaso 40 bisa dari na daukacin al’ummarsu alluran riga-kafin, kafin karshen shekarar da ta gabata, inda Rwanda ta zama daya daga cikin kasashen Afirka kalilan da suka kammala wannan aiki.

Alkaluman cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Afirka, wato African CDC, sun nuna cewa, zuwa ranar 29 ga watan karshe na shekara ta 2021, kaso 9.11 bisa dari kacal na daukacin al’ummar Afirka ne suka karbi alluran riga-kafin.

A nasa bangaren kuma, shugaba Paul Kagame na Rwanda, ya yi jawabi a ranar 27 ga watan Disambar bara, inda ya ce yiwa daukacin al’ummar kasar alluran, wata muhimmiyar hanya ce da ake bi wajen kare mutanen kasar. Ya kara da cewa, kawo yanzu, daga cikin ‘yan kasa da suka haura shekaru 12 da haihuwa, kaso 80 bisa dari sun karbi alluran riga-kafin akalla sau daya.

Tun lokacin da cutar ta barke a Rwanda, kasar Sin ta fara goya mata baya wajen yakar ta. A watan Nuwambar bara, gwamnatin kasar Sin ta mikawa Rwanda kashi na biyu, na alluran riga-kafin kyauta. (Murtala Zhang)