logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Uzbekistan sun taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldarsu

2022-01-02 18:18:16 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Uzbekistan, Shavkat Mirziyoyev, a yau Lahadi sun yi musayar sakonnin taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Xi ya jaddada cewa, yana dora muhimmanci matuka game da cigaban huldar dake tsakanin kasashen Sin da Uzbekistan, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Mirziyoyev don yin amfani da damar cika shekaru 30 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu a matsayin wata damar bude sabon shafi a tarihin cigaban muhimmiyar huldar dake tsakanin Sin da Uzbekistan, domin amfanawa kasashen biyu da kuma al’ummunsu.

A nasa bangaren, Mirziyoyev ya bayyana cewa, bangaren Uzbekistan a shirye yake ya kara zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da bunkasa kyakkyawar huldar abokantaka daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu domin kaiwa ga sabon matsayi a tarihin huldarsu.(Ahmad)