logo

HAUSA

‘Yan sanda sun ceto yara 21 da aka yi garkuwa dasu a arewa maso yammacin Najeriya

2022-01-02 18:11:44 CRI

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa, ta kubutar da yara 21 daga hannun ‘yan fashin daji da suka yi garkuwa da su a babbar hanyar mota a jahar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar, bayan sun yi musayar wuta da barayin dajin.

Mohammed Shehu, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara, ya bayyanawa taron manema labarai a Gusau, babban birnin jahar cewa, ‘yan sandan sun samu kiran waya mai tayar da hankali a daren Juma’a, inda aka sanar da su cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun datse babbar hanyar mota a kusa da kauyen Kucheri a karamar hukumar Tsafe dake jahar, inda suka yi garkuwa da matafiya da ba san adadinsu ba cikin wasu motoci biyar.

Shehu ya ce, an gaggauta tura jami’an ‘yan sanda zuwa yankin inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar, kana sun yi nasarar ceto yara 21 wadanda ke kan hanyarsu ta komawa makarantarsu da ke jahar Katsina, inda ‘yan fashin suka kai harin.

Kakakin ‘yan sandan ya ce, wasu mutanen da ba a bayyana adadinsu ba ciki har da malamin yaran da direban motar, a halin yanzu suna hannun masu garkuwar.

Shehu yace, hukumar ‘yan sanda ta tura karin dakaru domin tallafawa jami’an tsaron hadin gwiwa dake gudanar da aikin kubutar da ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kokarin damke maharan.(Ahmad)