logo

HAUSA

Gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta yi tir da rikicin da ya auku yayin zanga-zanga a kasar

2022-01-01 15:52:26 CRI

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan, ta yi tir da rikicin da ya auku yayin zanga-zangar ranar Alhamis, wanda ya kai ga mutuwar mutane 4 da raunata daruruwa.

Cikin wata sanarwa, gwamnatin ta ba hukumomi umarnin daukar dukkan matakan da suka dace da shari’a da aikin soji, wajen kare sake aukuwar makamancin lamarin, tare da tabbatar da an hukunta dukkan wadanda ke da hannu wajen tada rikicin.

An kashe masu zanga-zanga 4, yayin da wasu 297 tare da ‘yan sanda 49 suka jikkata a Omdurman.

Omdurman ne birnin kasar Sudan mafi yawan al’umma dake da mazauni a gabar yammacin kogin Nilu, daura da Khartoum, babban birnin kasar.

‘Yan sanda na zargin wasu masu zanga zanga da kulla makarkashi domin kai musu hari. Dubban masu zanga-zanga ne dai suka fantsama kan titunan Khartoum da sauran biranen kasar a ranar Alhamis. (Fa’iza Mustapha)