logo

HAUSA

Yankin ciniki cikin ‘yanci mafi girma a duniya zai bunkasa ci gaban tattalin arzikin duniya

2022-01-01 15:17:27 CRI

Yankin ciniki cikin ‘yanci mafi girma a duniya zai bunkasa ci gaban tattalin arzikin duniya_fororder_rcep

A rana ta farko ta sabuwar shekarar 2022, yarjejeniyar kawancen tattalin arziki ta RCEP ta fara aiki a hukumance, wadda ita ce irinta dake da mafi yawan al’umma da karfin tattalin arziki da cinikayya, haka kuma wadda ke da gagarumar damar raya duniya. Yarjejeniyar ta mamaye mutane biliyan 2.2, adadin da ya dauki kaso kimanin 30 na alkaluman GDP na duniya. Kashin farko na kasashen da suka shiga yarjejeniyar ya hada da kasashe 6 na ASEAN da kasashe 4 da suka hada da Sin da Japan da New Zealand da Australia.

Bayan yarjejeniyar ta fara aiki, sannu a hankali za a soke haraji kan kaso 90 na kayayyakin yankin. Baya ga haka, yarjejeniyar ta tanadi ingantattun ka’idoji a bangaren cinikayya da zuba jari da hakkin mallakar fasaha da cinikayya ta intanet da sauransu, wadanda ke nuna cewa, cikakkiyar yarjejeniya ce ta zamani dake burin habaka tattalin arziki da cinikayya da kuma moriyar juna.

A bangaren kasar Sin, yarjejeniyar RCEP wata sabuwar nasara ce wajen bude kofa ga kasashen waje da cika alkawarinta na ci gaba da bude kofar. Matakin bude kofa na yarjejeniyar a fannoni daban daban kamar na cinikayyar kayayyaki da zuba jari da ka’idoji sun dara matakin da WTO ta yi wa kasar Sin alkawari. Wannan ba sabon kuzari da zai karawa tattalin arzikin Sin ba, har ma da samar da sabon dandali ga yayata moriyar ci gaban kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)