logo

HAUSA

Kasar Sin mai juriya da ci gaba albarka ce ga duniya

2022-01-01 19:43:21 CRI

Kasar Sin mai juriya da ci gaba albarka ce ga duniya_fororder_sin

Bayan sauraron jawabin sabuwar shekarar 2022 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, Higvie Hamududu, shugaban jam’iyyar National Party ta Zambia, ya ce ya amince da sakon da jawabin ya kunsa. Ya ce kasar Sin ta ceto miliyoyin mutane daga kangin talauci, kuma ya kamata dukkanin kasashen duniya su yi koyi da dabarun ci gaba irin na kasar.

Ya ce kawo yanzu, kasar Sin ta samar da alluran rigakafin COVID-19 biliyan 2 ga kasashe da hukumomin duniya 120.

Ya ce daga gabatar da shirye-shiryen ci gaba zuwa yayata shawarar ziri daya da hanya daya, kasar Sin tana ci gaba da kokarin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama. (Fa’iza Mustapha)