logo

HAUSA

Masanin MDD: Sin ta jagoranci duniya wajen farfado da tattalin arziki da cinikayya a 2021

2022-01-01 15:47:13 CRI

Masanin MDD: Sin ta jagoranci duniya wajen farfado da tattalin arziki da cinikayya a 2021_fororder_liang guoyong

Liang Guoyong, babban masanin tattalin arziki na zauren MDD kan cinikayya da harkokin ci gaba, ya ce kasar Sin ta jagoranci duniya wajen farfado da tattalin arziki da cinikayya a shekarar 2021.

Liang Guoyong, ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta CMG ta kasar Sin, inda ya ce a bara, harkokin cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje, sun ci gaba da samun tagomashi. Dalilin haka shi ne domin farfadowar tattalin arzikin duniya, da tashin farashin kayayyaki, da matukar bukatar kayayyakin a manyan kasashe, da fifikon da Sin ke da shi a wajen tsarawa da aiwatar da tsarin cinikayya ta intanet da sarrafa kayayyaki da ababen more rayuwa da kuma dabaru.

Ya kara da cewa, bayan tattalin arzikin duniya ya samu koma baya da sama da kaso 3 a 2020, an sa ran samun ci gaba na kusan kaso 6 a 2021. Yana mai cewa, irin wannan farfadowar da tattalin arzikin duniya ya yi, na da alaka da tasirin tattalin arzikin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)