logo

HAUSA

Sin ta zama kasa mafi gudanar da aikin binciken sararin samaniya a duniya a shekarar 2021

2021-12-31 10:55:36 CRI

Sin ta zama kasa mafi gudanar da aikin binciken sararin samaniya a duniya a shekarar 2021_fororder_211231-Ahmad 2-China space launches

Hukumar kula da ayyukan binciken sararin samaniya da kimiyya da fasaha ta kasar Sin CASC, ta sanar da cewa, kasar Sin ta kaddamar da ayyukan binciken sararin samaniya kimanin 55 a shekarar 2021, kuma wannan adadin ya sa kasar ta zama ta farko dake sahun gaba a duniya.

Daga cikin ayyukan, an yi nasarar harba na’urar daukar tauraron dan adam guda 48 samfurin Long March. Kana ayyukan sun kuma kunshi harba na’urar binciken sararin samaniya hudu samfurin Kuaizhou-1A, da wani samfurin CERES-1 guda, da wasu guda biyu samfurin SQX-1.

A cewar hukumar ta CASC, a wannan shekarar an gudanar da ayyukan harba na’urar binciken sararin samaniya samfurin Long March karo na 400, wanda hakan ya nuna nasarar da kasar Sin ta cimma na karfafa ayyukan binciken sararin samaniya da kuma bunkasuwar fannin kimiyya da fasahar kasar. (Ahmad)