logo

HAUSA

MDD: An kwashe masu neman mafaka 177 daga Libya zuwa Nijer

2021-12-31 11:08:29 CRI

MDD: An kwashe masu neman mafaka 177 daga Libya zuwa Nijer_fororder_211231-Ahmad3-asylum seekers evacuated from Libya to Niger

Babban kwamishinan hukumar kula da ’yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ya bayyana cewa, an kwashe masu neman mafaka 177 daga kasar Libya zuwa jamhuriyar Nijer.

A cewar sanarwar, wannan shi ne karo na 30 da aka gudanar da aikin kwashe mutanen ta jiragen sama zuwa kasar Nijer tun bayan kaddamar da shirin gaggawa na kwashe mutanen dake gararamba a kasar Libya.

UNHCR ta sanar cewa, shirin wanda gwamnatin Nijer ta bullo da shi a shekarar 2017, inda ta amince za ta karbi mutanen dake neman mafaka a yankunan kasarta na wucin gadi da ’yan gudun hijirar da rayuwarsu ke fuskantar barazana a kasar Libya.

Ya zuwa yanzu, jimillar ’yan gudun hijira 3,710 da masu neman mafaka aka kwashe daga Libya zuwa Nijer, daga cikin adadin mutane 3,255 sun riga sun koma kasashensu na asali domin sake zaman rayuwa ko kuma samun halastaccen wurin zama na wucin gadi. (Ahmad Fagam)