logo

HAUSA

Burin jagoran kauye

2021-12-31 18:04:14 CRI

Burin jagoran kauye_fororder___172.100.100.3_temp_9500032_1_9500032_1_1_efe4705f-9fe4-4da7-baa7-c5e1cb461ae8

Gaoxigou wani kauye ne da ke gundumar Mizhi na lardin Shaanxi a arewa maso yammacin kasar Sin, duk da karancin ruwa da ake fama da shi a kauyen, bisa kokarin da aka yi na inganta muhallin wurin, ni’imar kauyen ta karu, har ma a lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki kauyen a watan Nuwamban shekarar 2021, ya yabawa kauyen kan yadda ya kasance abin misali wajen inganta muhalli.

Sai dai kauyen ba haka yake ba a shekarun 1950, wanda aka siffanta shi a matsayin “wurin da babu kome sai duwatsu”, inda ake ta fama da bala’u, don haka, zancen samun girbi mai kyau ma bai taso ba. Don ganin an magance matsalar abinci, mazauna kauyen sun fara kokarin inganta muhallin kauyensu, inda hakarsu ta cimma ruwa. Yanzu haka kauyen ya zamanto wurin da dazuzzuka da ciyayi suka game kaso 70% na fadinsa.

A wannan kauyen, akwai wata ka’idar da ake martabawa, wato duk wanda ke son shiga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ban da cika sharudan da aka gindaya, dole ne ya dasa bishiyoyi a kalla 100, tare da tabbatar da cewa, sama da kaso 90% daga cikinsu sun rayu. Mr. Jiang Liangbiao, sakataren jam’iyyar kwaminis reshen kauyen ya ce, “Ya kamata a yayata al’adar kiyaye muhalli da dasa bishiyoyi a kauyen, dalilin da ya sa muka bukace su dasa bishiyoyi shi ne, fahimtar da su muhimmancin kiyaye muhalli.”

A cikin ’yan shekarun baya, kauyen Gaoxigou ya kuma mai da hankali a kan aikin noman tufa da shinkafa a kan duwatsu da sauran amfanin gona, ayyukan da ya sa matsakaicin kudin shigar da mazauna kauyen kowanensu ke samu, ya kai kudin Sin yuan 18,851, wanda har ya zarce matsakaicin kudin shigar mazauna gundumar Mizhi.

A lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki kauyen a watan Nuwamban shekarar 2021, ya nuna yabo ga kauyen kan yadda ya kafa misali wajen inganta muhalli.

Mr. Jiang Liangbiao ya ce, yanzu haka kauyen yana kuma kokarin bunkasa ayyukan gona na zamani tare da bunkasa harkokin yawon shakatawa, kuma ana sa ran kudin da aka samu a shekarar 2021 a fannin harkokin yawon shakatawa, zai kai dubu 200. Ya ce, “Kamata ya yi mu yi gyare-gyare da kirkire-kirkire, mu kuma yi kokarin bunkasa tattalin arziki tare da kiyaye muhalli.” (Lubabatu Lei)