Kudin da Amurka ke kashewa a fannin soja ya sa ta zama babbar barazana ga zaman lafiya a duniya
2021-12-30 19:34:43 CRI
Kwanan nan ne shugaban Amurka Joe Biden, ya sanya hannu kan dokar tsaro ta kasa na kasafin kudin shekarar 2022, ya kuma kayyade cewa, kudaden tsaro da Amurkar za ta kashe a sabuwar shekarar 2022, zai kai dalar Amurka biliyan 768.2, wanda shi ne mafi yawan kudaden da Amurka ke kashewa a fannin aikin soja, tun bayan yakin duniya na biyu. Wannan ya sake fallasa kasar mai kwadayin shiga yaki da son mallakar makamai, Ya kuma kara tabbatar da cewa, Amurka ita ce babbar barazana ga zaman lafiyar duniya.
Bugu da kari, kudirin yana cike da tunanin yakin cacar baka, da kyamar akida. Abin da Amurkar ta kira wai "martani ga kalubalen kasar Sin" ba komai ba ne illa neman uzuri da ya wajaba ga Amurka, wajen kara yawan kudaden da take kashewa a fannin soji da fadada karfinta na soja.(Ibrahim)