logo

HAUSA

Cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan ta gudanar da ayyukan harba taurarin dan Adam har 22 a wannan shekara

2021-12-30 11:37:01 CRI

Cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan ta gudanar da ayyukan harba taurarin dan Adam har 22 a wannan shekara_fororder_810a19d8bc3eb135c6ba2cddc36c0edafc1f44d7

A jiya Laraba, an harba tauraron dan Adam na Tianhui-4, daga cibiyar harba taurarin dan Adam da ke birnin Jiuquan na kasar Sin, wanda ya kasance karo na 22 da cibiyar ta gudanar da wannan aiki a wannan shekara, wanda hakan ya kafa sabon tarihi a kasar, ta fannin yawan harba taurarin dan Adam da wata cibiyar harba taurarin dan Adam ta yi.

Ban da haka, a wannan shekara, cibiyar ta Jiuquan a karo na farko, ta gudanar da aikin harba kumbo mai dauke da mutane har sau biyu, kuma a karo na farko, ta gudanar da aikin dawo da kumbo mai dauke da mutane, matakin da ya sa cibiyar ta kafa sabon tarihi a fannoni da dama na nazarin sararin samaniya.

An ce, a shekarar 2022 mai zuwa, cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan, za ta gudanar da aikin harba kumbuna da dawowa da su sau biyu, baya ga kuma ayyukan harba tauraron dan Adam sama da 20. (Lubabatu)