logo

HAUSA

Najeriya na ban kwana da shekarar 2021 mai cike da kalubale tare da fatan farfadowa a badi

2021-12-30 10:45:46 CRI

Shekakar nan ta 2021 dake daf da kammala na cike da kalubale ga Najeriya, ciki har da kalubalen tsaro da ya jima yana addabar wasu yankunan kasar, yayin da kuma cutar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

A bana, Najeriya ta fuskanci hare-haren ’yan bindiga, ciki har da hari kan makarantu, da yin garkuwa da dalibai, an kuma kaddamar da hare-hare kan ofisoshin ’yan sanda, da gidajen yari, wadanda suka haifar da rasuwar jami’an tsaro da dama, kana wasu fursunoni suka tsere.

Najeriya na ban kwana da shekarar 2021 mai cike da kalubale tare da fatan farfadowa a badi_fororder_211230-Nigeria bids farewell to challenging 2021 as optimism grows for new year-Saminu

Yayin wani taro na kungiyar ECOWAS da ya gudana a baya bayan, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, kasar na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, wanda ke barazana ga dimokaradiyyar kasar. Ya ce karuwar rashin daidaito, da tashe-tashen hankula a kasar na da ban tsoro, don haka akwai bukatar abokan huldar kasar su tallafawa kokarin mahukuntan ta, wajen shawo kan matsalar tsaro da ta’addanci.

Duk da haka, an cimma wasu nasarori a fannin rage aukuwar tashe tashen hankula a kasar, musamman a bangaren dakile tsattsauran ra’ayi a yankin arewa maso gabas, wanda shi ne tungar kungiyar Boko Haram, da takwararta ta ISWAP.

Farfesa Sheriff Ghali, malami a jami’ar Abuja fadar mulkin Najeriya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin wata tattaunawa a kwanan baya cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar ta kara azama, wajen yin hadin gwiwa da abokan huldar ta na kasa da kasa, da sassa masu zaman kansu, da daidaikun mutane masu ruwa da tsaki a kasar, domin tsara matakan shawo kan kalubalen tsaro.

Najeriya na ban kwana da shekarar 2021 mai cike da kalubale tare da fatan farfadowa a badi_fororder_211230-Nigeria bids farewell to challenging 2021 as optimism grows for new year-Saminu-hoto2

Masana a fannin tattalin arziki a Najeriya, na ganin har yanzu akwai kyakkyawan fata, duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, da ma yaduwar cutar COVID-19 dake fadada a sassan kasar.

Wani hasashe na cibiyar Afrinvest mai bincike a fannin tattalin arziki, ya nuna cewa, tattalin arzikin Najeriya zai fadada da kaso 2.79 bisa dari, zuwa karshen shekarar nan ta 2021. Adadin da ya karu da kusan kaso 5 bisa dari, ragin da ya kai na kaso -1.79 bisa dari, idan an kwatanta da ma’aunin karuwar GDPn kasar na shekarar 2020, lokacin da kullen annobar COVID-19 ya yi tasiri ga yanayin tattalin arzikin kasar.

A karshen watan Oktoban 2021, Najeriya ta cimma muhimman nasarori, a fannin bunkasa sashen hada hadar kudade, lokacin da ta zama kasa ta farko a Afirka, da ta fara kaddamar da kudin internet da aka yiwa lakabi da eNaira.

Masana a fannin tattalin arzikin kasar sun ce, hakan zai taimaka wajen ingiza kirkire kirkire, da kara inganta sashen, tare da maida hankali ga dabarun hada hadar kudade ta amfani da na’urorin latironi.