Yancin 'yan jarida ba makami ne na siyasa da Amurka da kasashen Yamma za su yi amfani da shi wajen tayar da hargitsa a HK ba
2021-12-30 21:40:09 CRI
Dangane da matakin da 'yan sandan yankin Hong Kong na kasar Sin suka dauka a kan kafar yada labarai ta intanet mai suna "Stance News", sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Brinken, ya fitar da wata sanarwa jiya Laraba, inda ya yi ikirarin cewa, wai kasar Sin tana lalata 'yancin 'yan jarida a yankin Hong Kong.
Hong Kong al'umma ce dake rayuwa a karkashin doka, kuma 'yancin mutanen Hong Kong da suka hada da 'yancin fadin albarkacin baki da na 'yan jarida, duka suna da tabbacin kamar yadda doka ta tanada. A sa'i daya kuma, dokar da ta shafi manyan laifuffuka ta Hong Kong, ta nuna karara cewa duk wanda ya wallafa kalamai masu tayar da hankali, doka za ta yi aiki a kansa. Ra'ayyoin jama'a a Hong Kong baki daya, sun yi imanin cewa, matakin da 'yan sanda suka dauka kan "Stance News" ya yi daidai da doka, kuma ba shi da alaka da abin da ake kira wai 'yancin aikin jarida."(Ibrahim)