logo

HAUSA

Amurka Ta Yi Amai Ta Lashe

2021-12-29 16:08:54 CRI

Amurka Ta Yi Amai Ta Lashe_fororder_1

Daga Ibrahim Yaya

A baya Amurka ta siyasantar da batun gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da birnin Beijing zai karbi bakunci a shekarar 2022 dake shirin kamawa, inda ta sanar da cewa, wai ba za ta turo jami’anta zuwa gasar ba tare da an gayyace su ba, ta hanyar fakewa da batun ’yanci da kare hakkin bil-Adama a yankin Xinjiang na kasar Sin, wanda yin hakan tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar ta Sin.

Ana haka kuma, sai kwatsam a ranar Litinin din nan, Amurkar ta ce ta shirya aika wata tawagar jami’an gwamnatinta zuwa kasar Sin, a lokacin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, har ma ta gabatar da takardun neman iznin shiga kasar. Kan wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, kasar Sin za ta bi ka'idojin kasa da kasa da suka dace da dokoki da manufofin da abin ya shafa, na ramawa kura aniyarta.

Bayan da Amurka ta yi kidanta ta kuma yi rawarta game da batun kin tura jami’anta da ta furta a baya da ma janye wannan ikirari daga bisani, sai kuma ta sake neman siyasantar da gasar, inda a kwanakin baya ta bukaci kasar Sin, da wai kada ta takaita 'yancin zirga-zirga ga 'yan jaridu a lokacin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, tare da tabbatar da kare lafiyarsu da 'yancin bayar da rahotanni. Hali aka ce zanen dutse.

Rahotanni na nuna cewa, yanzu haka 'yan jarida fiye da 2,500 ne suka mika takardarsu na neman rajista, don watsa rahotanni game da gasar Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing. Don haka, wannan batu da Amurka ta gabatar bai ma taso ba.

Kasar Sin dai ta sha nanata cewa, tana maraba da 'yan jaridu, da su rika ba da sahihan rahotannin game da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing a dukkan fannoni, da kuma gudanar da aikin sa ido, wanda zai taimaka matuka wajen inganta tsari da gudanar da wannan gasa cikin armashi.

Sai dai kuma, duk da cewa, yanzu Amurka ta yanke shawarar tura jami’anta zuwa gasar, kasar Sin ta yi kakkausar suka ga yadda wasu kasashe ke neman siyasantar da wasannin motsa jiki, da akidar nuna kyama ga kasar Sin, da kirkirar labarai da bayanan karya da ke bata sunan kasar Sin da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing da sunan 'yancin 'yan jarida ko wata manufa ta neman kiyaye moriya da ta saba ka’ida.

Tuni dai kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya IOC, ya yi matukar yabawa kasar Sin bisa cika alkawarinta na gayyatar dukkan kasashe dake martaba ruhin gasar, da gudanar da wasanni ba tare da gurbata muhalli ba, ta hanyar amfani da makamashi masu tsafta a wuraren wasannin, tare da jan hankalin masoya wasannin lokacin hunturu miliyan 300. Yanzu ya rage ga kasashe ’yan koren Amurka da su ma suka ce ba za su tura jami’ansu don halartar gasar ta Beijing ba, da su fahimci gaskiya su daina yarda ana yaudararsu domin kawai neman kare wata moriya da ba za ta taba haifar da da mai ido ba. (Ibrahim Yaya)