logo

HAUSA

Sin ta fidda takardar bayani ta farko game da aikin kula da fitar da kayayyaki

2021-12-29 13:42:35 CRI

Sin ta fidda takardar bayani ta farko game da aikin kula da fitar da kayayyaki_fororder_211229-Ahmad 3-white paper

A yau Laraba, kasar Sin ta fidda takardar bayani ta farko game da tafiyar da aikin fitar da kayayyaki domin samar da cikakken tsari dake shafar manufofin da za su taimakawa al’ummun kasa da kasa wajen fahimtar hakikanin matsayar kasar.

Takardar mai taken “Tafiyar da aikin fitar da kayayyaki na kasar Sin" da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fiar, ta yi cikakken bayani game da matsayar kasar Sin, da hukumominta, da kuma tsarinta na inganta tafiyar da ayyukan fitar da kayayyaki, kana da manufofin kasar na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaban duniya, da tabbatar da tsaro a matakin kasa da kuma matakan kasa da kasa.

Takardar bayanin ta kuma jaddada cewa, yin adalci, da tunani mai kyau, da rashin nuna banbanci game da matakan dake shafar gudanar da aikin fitar da kayayyaki suna da matukar muhimmanci game da shawo kan matsalolin barazanar tsaro na kasa da kasa da na shiyya da kuma kalubaloli da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaban duniya.

Kasar Sin tana kokarin daukar dukkan matakai na tabbatar da tsaron kasa, kana tana daukar karin matakai da nufin daga matsayin tabbatar da shirin dunkulewar tattalin arzikin duniya, a cewar takardar.

Domin kara gina tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa da kuma tabbatar da karin zaman lafiyar kasar Sin, kasar ta jajurce don cimma muhimmin tsarin cudanya mafi inganci a tsakanin kasa da kasa da kuma tabbatar da tsaro, da zamanintar da aikin lura da fitar da kayayyaki, kana da bude sabon shafin cigaba game da gudanar da aikin fitar da kayayyaki, in ji takardar bayanin.

Takardar bayanin ta ce, kasar Sin za ta sauke nauyin dake bisa wuyanta a matakin kasa da kasa, za ta sa lura wajen kokarin sauke muhimman hakkokin kasa da kasa dake bisa wuyanta, kana za ta kara daga matsayin huldar dake tsakaninta da kasa da kasa.

A cewar takardar bayanin, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai wajen shiga harkokin kasa da kasa don tafiyar da ayyukan fitar da kayayyaki, da samar da gagarumin ci gaba dake shafar tsare-tsaren kasa da kasa dake shafar wannan fanni, kana za ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya wajen gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma da gabatar da ingantaccen tsari mai karfi na bunkasa zaman lafiya da ci gaban duniya. (Ahmad)