logo

HAUSA

Afrika Na Bukatar Taimako Na Gaske A Maimakon Kyautar Alluran Rigakafin Da Wa’adin Aikin Su Ya Kusan Karewa

2021-12-29 17:28:05 CRI

Afrika Na Bukatar Taimako Na Gaske A Maimakon Kyautar Alluran Rigakafin Da Wa’adin Aikin Su Ya Kusan Karewa_fororder_9d82d158ccbf6c8107765b4f82fd123c32fa4024

Afrika Na Bukatar Taimako Na Gaske A Maimakon Kyautar Alluran Rigakafin Da Wa’adin Aikin Su Ya Kusan Karewa_fororder_d8f9d72a6059252d1159918101149d325ab5b906

Daga Amina Xu

Kwanan baya, Najeriya ta lalata alluran rigakafin COVID-19 na AstraZeneca sama da miliyan daya, wadanda aka tattaro daga sassan kasar bayan da aka gano wa’adin amfanin su ya kusa karewa. Kasashen Afrika na matukar bukatar alluran, amma wasu kasashen yamma sun ba su alluran da wa’adinsu ya kusan karewa. Abin da ya nuna cewa, gibin samun isashun alluran dake tsakanin kasashen yamma da kasashe masu tasowa ya kara habaka, kuma abin bakin ciki ne ganin yadda wadannan alluran suka lalace, mutane da dama sun rasa damar samun alluran saboda hakan.

Shugaban hukumar bunkasa kiwon lafiyar al’umma a matakin farko ta kasar (NPHCDA) Faisal Shuaib ya bayyana fushinsa na cewa, abin ya bayyana manufar rarraba allura bisa bambancin ra’ayin al’umma. Kasashe masu wadata suna mallakar fasahar samar da rigakafi, amma sun jibge alluran rigakafi har su baiwa kasashen Afrika lokacin da wa’adinsu ya kusan karewa, wasu wa’adinsu da ya rage ya kai makonni biyu kawai.

Najeriya ba ita kadai ce ta fuskanci wannan matsala a Afrika ba. Tun daga watan Yuni na bana, WHO ta ba da kididdigar cewa, kasashe 8 sun fuskanci wannan matsala. Malawi, da Sudan ta kudu da sauransu na cikin kasashen da suka lalata dubun-dubatar alluran. Sau da dama ne WHO da sauran kungiyoyin kasa da kasa, sun yi kira ga kasashen yamma, da su taimakawa kasashen Afrika wajen dakile cutar tare, amma sai kasashen yamma sun samarwa kasashen Afrika alluran da wa’adinsu ya kusan karewa, matakin da ba zai bayyana niyyarsu na hadin kan kasa da kasa na dakile cutar ba. Abun tambaya shi ne, shin ko kasashen yamma sun yi hakan ne domin musanta ra’ayin nuna bambancin ra’ayin al’umma wajen rarraba allurai da suke dauka ne?

Sabanin yadda kasashen yamma suka yi, ya zuwa karshen watan Nuwamba, Sin ta samarwa kasashen Afrika alluran kimanin miliyan 180, wadanda suke shafar dukkanin kasashen Afrika. A taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi ba da dadewa ba, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta baiwa Afirka karin wasu alluran rigakafi biliyan 1. Haka kuma, wa’adin allurar rigakafin da aka samar a kasar Sin gaba daya, za su kai shekaru 2 zuwa 3, kuma ba sa bukatar wani yanayi na musamman na sufuri, ko yadda za a ajiye su, wanda hakan ya dace da bukatun kasashe masu karami da matsakaicin kudin shiga. Abin da ya nuna cewa, tun daga farkon aikin nazarin alluran, Sin ta yi shirin baiwa kasashe masu tasowa taimako.

WHO ta taba yin kira da a kawo karshen yaduwar cutar COVID-19 kafin karshen shekarar 2022, kuma rigakafi mataki ne mafi dacewa na cimma wannan buri. Amma kawo yanzu, kashi 7.5% daga cikin gaba dayan al’ummar Afrika biliyan 1.3 kacal ne aka yiwa cikakkun allurai. A bangare guda kuma, wasu kafofin yada labarai na Amurka na ba da labarai cewa, yawan alluran da Amurka ta lalata ya fi yawansu da wasu kasashe masu tasowa suke bukata. Nuna halin ko in kula ga yaduwar cutar a sauran wurare da Amurka ke yi, ba zai taimakawa WHO wajen cimma burin kawo karshen yaduwar cutar kafin karshen shekarar 2022 ba, kuma hanya daya tilo da za a bi, ita ce hadin kan kasa da kasa. Kasashen Afrika ba cibiyar lalata alluran rigakafin kasashen yamma da wa’adinsu ya kusan karewa ba ne, a maimakon haka, suna bukatar taimako bisa sahihanci. (Amina Xu)