logo

HAUSA

Zambia ta kaddamar da tsarin bunkasa yawon bude ido na cikin gida

2021-12-29 10:35:20 CRI

Zambia ta kaddamar da tsarin bunkasa yawon bude ido na cikin gida_fororder_211229-Saminu 2-Zambia

Mahukunta a kasar Zambia sun kaddamar da wani sabon shirin bunkasa yawon shakatawa tsakanin al’ummun kasar, a wani mataki na kare fannin daga durkushewa baki daya, bayan da annobar COVID-19 ta yi matukar haifar da koma baya ga fannin.

Da yake tsokaci yayin kaddamar da shirin a jiya Talata, ministan ma’aikatar bunkasa yawon shakatawa da raya al’adu na kasar Rodney Sikumba ya ce, shirin zai ba da damar tallafawa fannin yawon bude ido na cikin gida, yayin da tafiye-tafiye tsakanin kasa da kasa suka yi matukar raguwa. Zai kuma karfafa gwiwar ’yan kasar wajen ziyartar wuraren yawon bude ido don raya fannin.

Rodney Sikumba ya ce, za a aiwatar da manufofin dinke sassan raya fannin, ta yadda kasar za ta rika cin gajiya, da kuma fadada hada hadar yawon bude ido yadda ya kamata.

Har ila yau, shirin ya tanaji tsarin tallafawa kamfanoni masu ruwa da tsaki, a fannin yawon shakatawa, da dokoki, da hanyoyin ba da rangwame, ta yadda za su samu ci gaba.

Tuni dai ma’aikatar ta fara aiwatar da wani shiri na daga matsayin ababen more rayuwa, da suka hada da samar da hanyoyin mota, da kyautata filayen jiragen sama, da sauran abubuwan da ake bukata, don cimma nasarar manufar da aka sanya gaba.

Har ila yau, ana sa ran daukar wannan mataki zai karfafa gwiwa ga masu sha’awar zuba jari a sassan yawon shakatawa daban daban dake kasar ta Zambia.  (Saminu)