logo

HAUSA

Mutane 38 sun mutu a mahakar zinare a kudancin Sudan

2021-12-29 10:24:40 CRI

Mutane 38 sun mutu a mahakar zinare a kudancin Sudan_fororder_211229-Ahmad1-Kordofan Sudan

A kalla mutane 38 ne suka mutu bayan da ramin hakar zinare ya rufta da su a jihar West Kordofan dake kudancin kasar Sudan, kamfanin gwamantin kasar ne ya bayyana cikin wata sanarwa.

Mahakar zinaren ta rufta ne a kusa da garin El Nuhud dake jihar West Kordofan, mai tazarar kilomita 500 daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

A cewar kamfanin, a lokacin bayan gwamnatin jihar West Kordofan da hukumar tsaron jihar sun fidda sanarwar daukar matakin rufe wajen hakar ma’adanin, inda aka bayyana cewa wajen bai dace da aikin hakar ma’adanai ba.

To sai dai kuma, masu aikin hakar ma’adanan sun sake komawa wajen tare da ci gaba da aikin hakar ma’adanan duk da matakin haramcin da gwamnatin ta sanya.

Kimanin mutanen Sudan miliyan biyu ne ke aiki a kamfanonin hakar ma’adanai a tsarin gargajiya a duk fadin kasar ta Sudan, da suka hada da jihohin Red Sea, Nahr al-Neel, South Kordofan, West Kordofan da kuma Northern Kordofan.

A bisa ga alkaluman hukumomi, tsarin hakar ma’adanai na gargajiya yana bayar da gudunmawar kashi 75 bisa 100 na yawan zinaren da ake samarwa a Sudan, wanda ya zarce tan 93 a duk shekara. (Ahmad)