logo

HAUSA

Matakin Japan na neman zubar da ruwan dagwalaon tashar nukiliya a cikin teku kuskure ne da ba za a yafe ba

2021-12-29 19:49:21 CRI

Matakin Japan na neman zubar da ruwan dagwalaon tashar nukiliya a cikin teku kuskure ne da ba za a yafe ba_fororder_japan

Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara ta 2022, duniya kuma na fatan ganin gobe mafi kyau. Sai dai a baya-bayan nan, gwamnatin kasar Japan ta sanar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon tashar makamashin nukiliya ta Fukushima ta hanyar da ba ta dace ba.

Shin shawarar da Japan din ta yanke ta zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliya ta dace? Shin bayanan sun tabbata? Shin za a iya dogaro da na’urorin tace ruwan dagwalon? A cikin watanni takwas da suka gabata, kasashen duniya sun nuna damuwa matuka ga kasar Japan, amma bangaren Japan, ya yi kunnen uwar shegu da hakan, inda ya ci gaba da kirkiro karairayi da dabaru, da kuma ci gaba da inganta tsare-tsare na zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliyar a cikin teku, a kokarin mayar da kasashen dake yankin tekun Pacific girbar sakamakon abin da zai biyo baya. Babu shakka wannan ganganci ne da nuna son kai matuka.(Ibrahim)