logo

HAUSA

Yadda kasashen yamma ke tafiyar da allurar rigakafin da wa’adinsu ya kare a Afirka na cutar da kansu

2021-12-28 19:21:57 CRI

Yadda kasashen yamma ke tafiyar da allurar rigakafin da wa’adinsu ya kare a Afirka na cutar da kansu_fororder_疫苗-9

Ya zuwa karshen watan Nuwamba, kasar Sin ta samar da alluran rigakafi kusan miliyan 180 ga Afirka. A taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi ba da dadewa ba, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta baiwa Afirka karin wasu alluran rigakafi biliyan 1. Haka kuma, wa’adin allurar rigakafin da aka samar a kasar Sin gaba daya, za su kai shekaru 2 zuwa 3, kuma ba sa bukatar wani yanayi na musamman na sufuri ko yadda za a ajiye su, wanda hakan ya dace da bukatun kasashe masu karami da matsakaicin kudin shiga.

Afirka na bukatar taimako na hakika, maimakon mu'amala da gudummawar jebun rigakafin da wa’adinsu ya kare. Ya kamata kasashen yammacin duniya, su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu tare da baiwa Afirka alluran rigakafi masu inganci da yawa kamar kasar Sin. Matukar wata kasa ba ta kawar da annobar ba, to da wuya a ce duniya baki daya ta tsira. Lokacin da kasashen yamma ke taimakawa Afirka, hakika suna taimakon kansu ne. (Ibrahim)