logo

HAUSA

Kongo DRC za ta yi wa mutane miliyan biyu riga-kafin cutar kwalara

2021-12-28 11:40:18 CRI

Kongo DRC za ta yi wa mutane miliyan biyu riga-kafin cutar kwalara_fororder_211228-a02-DR Congo launches cholera vaccination campaign targeting 2 million people

Hukumomin lafiya sun sanar cewa, jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, ta kaddamar da gagarumin aikin allurar riga-kafin cutar kwalara inda ake fatan yiwa mutane miliyan biyu tsakanin ’yan shekara guda zuwa sama a larduna uku dake shiyyar gabashin kasar domin dakile yaduwar annobar.

Za a gudanar da gangamin aikin riga-kafin ne a lardunan Haut-Lomami, da South Kivu da kuma Tanganyika, su ne yankunan da annobar ta fi kamari tun bayan barkewar cutar a watan Agusta, kuma aikin zai shafi yankunan kiwon lafiya 13 na kasar yayin da aka tanadi allurai kusan miliyan 4 karkashin shirin yaki da cutar kwalara na kasa da kasa wato Global Task Force ya samar da alluran.

Kimanin ma’aikatan lafiya 3,600, da suka hada da jami’an aikin riga-kafin da masu wayar da kan al’ummar unguwanni, aka tura don gudanar da gangamin wanda za a shafe kwanaki shida ana gudanarwa.

Tun a farkon wannan shekarar, DRC ta bada rahoton mutane 8,279 da ake zaton sun kamu da cutar amai da gudawa, yayin da aka samu hasarar rayuka 153 a larduna 16 daga cikin lardunan kasar 26.

Wannan shi ne karo na biyu na gagarumin aikin riga-kafin da aka gudanar a DRC a wannan shekara. A watan Maris da Yuli, an yiwa sama da mutane miliyan 1.4 riga-kafin cutar kwalarar a shiyyar kudu maso gabashin lardin Haut-Katanga. (Ahmad)