logo

HAUSA

Sani Musa Babura: Ina son bada gudummawata ga harkokin lafiyar Najeriya

2021-12-27 13:41:07 CRI

Sani Musa Babura: Ina son bada gudummawata ga harkokin lafiyar Najeriya_fororder_微信图片_20211227134035

A wannan mako, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da wani dan asalin Jigawar Najeriya, wanda ya taba hira da shi wasu shekaru biyu da suka gabata, wato lokacin da yake karatu a kwalejin koyon ilimin likitanci dake birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. Sunansa Sani Musa Babura, wanda a yanzu haka yake aiki a asibitin koyarwa dake unguwar Nassarawa a Kanon Najeriya, ya yi tsokaci kan bambancin yanayin likitanci tsakanin Najeriya da kasar Sin, da burin da yake kokarin neman cimmawa, gami da kiransa ga al’umma. (Murtala Zhang)