logo

HAUSA

Shugaban babbar majalissar zartaswar Libya ya zargi majalissar wakilan kasar da haddasa dage zabe

2021-12-27 11:46:16 CRI

Shugaban babbar majalissar zartaswar Libya ya zargi majalissar wakilan kasar da haddasa dage zabe_fororder_211227-Libyan High State Council chief blames parliament-Saminu

Shugaban babbar majalissar zartaswar kasar Libya Khaled al-Meshri, ya zargi majalissar wakilan kasar da haddasa dage zaben shugaban kasa.

Al-Meshri wanda ya bayyana korafinsa a wani zama da majalissar ta yi a jiya Lahadi, ya ce gazawar majalissar wakilan na samar da hurumi a kundin mulkin kasar, da dokokin zabe, tare da halin ko in kula na hukumar gudanar da zaben kasar ne suka haifar da dage gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Jami’in ya ce, abun takaici ne ganin yadda sassan da suka gaza sauke nauyin dake wuyansu na gudanar da zaben, a yanzu ke musayar zargin koma bayan da suka haddasa.

A kwanakin baya ne dai hukumar zaben kasar, ta gabatar da shawarar dage babban zaben Libya daga ranar 24 ga watan Disambar nan zuwa 24 ga watan Janairun shekara mai zuwa.

Zabukan kasar Libya na cikin tsare-tsaren da aka tanada, karkashin shirin sulhun siyasa na kasar wanda MDD ke daukar nauyin aiwatarwa, wanda ke da nufin samar da daidaito a kasar, bayan shafe shekaru tana fama da matsalolin siyasa da tsaro.   (Saminu)