logo

HAUSA

Mahukuntan Isra’ila sun amince da gina karin matsugunan Yahudawa 2 a tuddan Golan

2021-12-27 11:54:37 CRI

Mahukuntan Isra’ila sun amince da gina karin matsugunan Yahudawa 2 a tuddan Golan_fororder_211227-Israel approves 2 new settlements-Saminu

Majalissar ministocin Isra’ila ta amince da gina karin sabbin matsugunan Yahudawa guda 2 a tuddan Golan, yankin da kasar ta kwace daga Syria a yakin gabas ta tsakiya na shekarar 1967.

Yayin taron ministocin da ya gudana jiya Lahadin a Golan, Isra’ila ta amince da kashe miliyoyin daloli, don gina gidaje da za su baiwa Yahudawa ikon fadada mazaunan su a yankin da ake takaddama a kansa.

Majalissar ministocin Isra’ila ta ce za ta gina rukunin gidajen Asif da Matar, masu kunshe da gidajen kwana kimamin 2,000 ko wannen.

Kaza lika, majalissar ta amince da kashe karin kimanin dalar Amurka miliyan 183 cikin shekaru 5 masu zuwa, domin gina sabbin gidaje 7,300 a garin Katzrin, da mazaunin majalissar gudanarwar Golan.

Fatan gwamnatin Isra’ila shi ne ninka adadin yahudawa mazauna garin Katzrin, tare da fadada yawan yahudawa mazauna kananan unguwanni a daukacin sassan mazaunin majalissar gudanarwar Golan.

Bayan amshe iko da Golan, Isra’ila ta hade yankin da sassan ta a shekarun 1980, ko da yake hakan bai samu amincewar sassan kasa da kasa ba. Kaza lika a ranar 5 ga watan Nuwambar shekarar bara, babban zaman MDD ya sake tabbatarwa Syria iko da tuddan Golan. (Saminu)