logo

HAUSA

Kasashen yamma sun baiwa kasashen Afirka alluran rigakafin da wa’adinsu ke gab da karewa

2021-12-27 20:36:00 CRI

Kasashen yamma sun baiwa kasashen Afirka alluran rigakafin da wa’adinsu ke gab da karewa_fororder_疫苗-7

Yau ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jagoranci taron manema labaran da aka saba shiryawa, inda wani dan jarida ya yi masa tambaya cewa, kamar yadda rahotanni suka nuna, a baya-bayan nan an tilastawa Najeriya lalata allurar rigakafin AstraZeneca miliyan 1.06. Kafofin yada labarai sun bayyana cewa, rigakafin da kasashen suka samu daga kasashen yamma, karkashin shirin COVAX, wa’adinsu zai kare ne cikin makonni 4-6 kawai lokacin da suka isa Najeriya, kuma ba za a iya amfani da su cikin lokaci ba. Mene ne ra'ayin kakakin kan wannan?

Zhao ya bayyana cewa, “Na lura da rahotannin da abin ya shafa, kuma kasashen Afirka kamar Senegal, da Malawi, da Kongo (DRC) su ma suna fuskantar matsalar karewar wa’adin rigakafin a matakai daban-daban.”

Zhao Lijian ya ce, kasar Sin ta dage wajen daukar allurar rigakafin cutar, a matsayin wani kaya na al’ummar duniya, da kuma samar da alluran rigakafi ga duniya, musamman kasashe masu tasowa. A halin da ake ciki yanzu, ana ci gaba da samun jinkiri da sake maimaita lamarin. Don haka, ana fatan kasashen da abin ya shafa, za su cika alkawuran da suka dauka, tare da samar da ingantattun alluran rigakafi ga kasashe masu tasowa, ciki har da Afirka, ta yadda za su ba da gudummawa da gaske, ta yadda baki dayan bil-Adam zai samu nasarar annobar nan da nan. (Ibrahim)