logo

HAUSA

Kamfanonin Sadarwar Sin Sun Shiga Shekarar 2021 Da Kafar Dama

2021-12-27 20:02:44 CRI

Kamfanonin Sadarwar Sin Sun Shiga Shekarar 2021 Da Kafar Dama_fororder_1

Daga Ahmad Fagam

Yayin da shekarar 2021 ke yin ban kwana, fannoni da dama na tattalin arzikin kasar Sin sun samu tagomashi, kuma tamkar abin da nan ne da masu hikimar magana ke cewa, “ko yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba.” Hakika za mu iya cewa kamfanonin sadarwar kasar Sin tamkar sun shiga shekarar 2021 mai karewa da kafar dama. Kamar yadda alkaluman da hukumomi suka fidda a karshen mako ya nuna cewa, kamfanonin sadarwar kasar Sin sun samu gagarumar bunkasar kudaden shigarsu a watanni 11 na farkon shekarar 2021. A bisa ga alkaluman, jimillar kudaden shigar kamfanonin ya karu da kashi 8.1 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wanda ya zarce yuan RMB triliyan 1.35, wato kwatankwacin dala biliyan 212 a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin ta bayyana. A cewar ma’aikatar, ya zuwa karshen watan Nuwamba, manyan kamfanonin sadarwar guda uku na kasar Sin, da suka hada da China Telecom, China Mobile da China Unicom, suna da yawan masu amfani a wayoyin hannu sama da mutane biliyan 1.64, adadin da ya karu da mutane miliyan 47.92 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara. Adadin masu amfani da wayoyin hannu na fasahar 5G ya kai miliyan 497, inda ya karu da mutane miliyan 298 daga karshen shekarar bara. Manyan kamfanonin sadarwar uku sun kuma samu karuwar adadin masu amfani da fasahar intanet mai saurin gaske ya zuwa karshen watan Nuwamba, inda adadin ya karu da mutane miliyan 51.85 daga karshen shekarar bara wanda adadinsu ya kai miliyan 535. Ko da yake, ba kamfanonin sadarwar kasar ne kadai suka samu wannan tagomashi ba, a karshen makon jiya cibiyar nazarin harkokin duniya, ta fitar da wani rahoto mai taken "Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin karkashin sabon tsarin raya kasa" a nan birnin Beijing. Rahoton ya nuna cewa, akwai kyakkyawar makoma na samun hadin gwiwa a duniya a fannin tattalin arziki na zamani, da tattalin arziki maras gurbata muhalli, da gina ababen more rayuwa, da cinikayyar hidimomi. A sa'i daya kuma, tattalin arzikin kasar Sin ya kara samar da zarafi ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa, wato abin nufi tattalin arzikin Sin ya samar da karin damar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Bugu da kari, rahoton ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwar kasa da kasa a fannin tattalin arziki, da cinikayya na kasar Sin, kuma ya yi nazari kan fannoni daban-daban a dukkan matakai tare da gabatar da sabbin dabaru, da damammakin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje a nan gaba. (Ahmad Fagam)