logo

HAUSA

Yau ce ranar cika shekaru 13 da sojojin ruwan Sin ke gudanar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwan gabar tekun Aden

2021-12-26 16:24:44 CRI

Yau ce ranar cika shekaru 13 da sojojin ruwan Sin ke gudanar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwan gabar tekun Aden_fororder_aden

Yau ranar 26 ga watan Disamba, rana ce ta cika shekaru 13 da sojojin ruwan kasar Sin suke gudanar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwan dake gabar tekun Aden da kuma Somaliya, a cikin wadannan shekarun 13, gaba daya rundunar sojojin ruwan kasar Sin ta aika ayarin jiragen ruwan yaki har sau 39, inda sojojin ruwan kasar suka gudanar da ayyukan ba da kariya da yawansu ya kai 1461 ga jiragen ruwa na kasar Sin da na ketare sama da dubu 7.

Gabar tekun Aden yana tsakanin tekun Indiya da tekun Red Sea ne, jiragen ruwan kasuwanci fiye da dubu goma ne sukan ketare shi a ko wace shekara, amma akwai hadari matuka a gabar tekun sakamakon yawan ‘yan fashin teku. A don haka sojojin ruwan kasar Sin sun fara gudanar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwan kafin shekaru 13 da suka gabata, har sun samu amincewa daga jiragen ruwan kasuwanci matuka.

Alkaluman da aka samar sun nuna cewa, cikin wadannan shekaru 13, gaba daya adadin jiragen ruwan da sojojin ruwan kasar Sin suka ceto ya kai sama da 70, kuma adadin jiragen ruwan ‘yan fashin tekun da suka kora ya kai kusan 3000, ko shakka babu, sojojin ruwan kasar Sin sun taka babbar rawa wajen tabbatar da tsaron hanyoyin cinikayyar kasa da kasa, tare kuma da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.(Jamila)