logo

HAUSA

Harin bam ya kashe mutane da dama a arewa maso gabashin jamhuriyar Kongo

2021-12-26 19:26:12 CMG

Harin bam ya kashe mutane da dama a arewa maso gabashin jamhuriyar Kongo_fororder_congo

Mutane masu yawa ne suka mutu kana wasu da dama sun samu raunuka a harin kunar bakin wake da ya faru da yammacin ranar Asabar, a yayin da ake tsaka da shagulgulan bikin kirsimeti a shiyyar arewa maso gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, kamar yadda gwamnatin Kongon ta tabbatar da faruwar lamarin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, bam din ya fashe ne da misalin karfe 7 na yamma agogon kasar, a birnin Beni, dake lardin Kivu, a daidai lokacin da ake gudunar da bukukuwan kirsimeti, lamarin da yayi sanadiyyar hasarar rayuka da dama.

Kakakin gwamnatin kasar Kongo Patrick Muyaya, ya wallafa a shafin twita cewa, gwamnatin kasar tayi Allah wadai da harin bam din na ranar kirsimeti a wata mashaya dake birnin Beni, wanda wani dan kunar bakin wake ya kai harin. Kuma an samu hasarar rayuka. Tuni aka tura jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ya faru.

Da yake jawabi ta gidan radiyon kasar ba tare da yin cikakken bayani kan fashewar bam din ba, magajin garin birnin Beni, ya umarci mutane dasu zauna a gidajensu don baiwa jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya damar gudanar da ayyukansu na kwashe mutanen da suka ji raunuka da kuma killace wajen da harin ya auku.(Ahmad)

Ahmad