logo

HAUSA

Kafar yada labarai: Masu zanga-zangar neman kafa mulkin farar hula a Sudan sun isa fadar shugaban kasar

2021-12-26 19:28:12 CMG

Kafar yada labarai: Masu zanga-zangar neman kafa mulkin farar hula a Sudan sun isa fadar shugaban kasar_fororder_sudan

A jiya Asabar masu zanga-zanga a Sudan sun cimma nasarar kaiwa ga fadar shugaban kasa dake Khartoum, babban birnin kasar, inda suke nema a tabbatar da kafa mulkin farar hula a kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar SUNA ya bada rahoto.

Masu zanga-zangar sun isa yankin da fadar mulkin kasar take, inda suke rera wakar nuna kin amincewa da yarjejeniyar siyasar da aka kulla tsakanin shugaban rikon kwarya na majalisar mulkin kasar, Abdel Fattah Al-Burhan, da firaministan rikon kwarya, Abdalla Hamdok.

Dubban fararen hular kasar Sudan ne suka gudanar da zanga-zangar a babban birnin kasar Khartoum da sauran biranen kasar a ranar Asabar.

Hukumomi a Sudan sun katse layukan sadarwa da kafofin intanet gabanin fara zanga-zangar ta ranar Asabar. A cewar shaidun gani da ido, an girke daruruwan sojoji da dakarun tsaro na ko-ta-kwana a mashigar babbar gadar da ta hade manyan biranen kasar uku, da suka hada da Khartoum, Omdurman, da Bahri.

A ranar Juma’a, kungiyar kwararrun kasar Sudan, wacce ke jagorantar zanga-zangar, sun bukaci al’ummar kasar dasu fito kwansu da kwarkwata don shiga zanga-zangar wacce aka tsara gudanarwa a ranar Asabar don neman kafa cikakkiyar gwamnatin fararar hula a kasar.(Ahmad)

Ahmad